Connect with us

LABARAI

2019: Ku Shirya Wa Yakin Kawar Da Buhari –Obasanjo

Published

on


Tsohon Shugaban kasarnan, Olusegun Obasanjo, ya kirayi wakilan kungiyar sa ta hadaka, ‘Coalition for Nigeria Mobement (CNM), a ranar Asabar da su shirya wa yakin batakashin fatattakan Shugaba Buhari, daga kujerar mulkin kasarnan, domin su amshe shugabancin kasarnan a shekarar zaben 2019. Ya karfafe su da su umurci duk wanda ya kai munzalin jefa kuri’a da ya tabbatar da katin jefa kuri’ar na shi yana hannun shi kafin lokacin zaben.

Obasanjo, ya fadi hakan ne wajen bukin kafa cibiyar kungiyar na shi ta Jihar Oyo, wanda aka yi a cibiyar shakatawa ta, Trans Amusement Park, da ke Ibadan, ya kuma neme su da ka da su gajiya, su kuma kuduri aniyar ceto Nijeriya, ka da kuma su razana da duk wani tsoratarwa da za a yi masu.

“Kowa ya sa a ransa aniyar ceton Nijeriya, aikin zai yiwu yana da wahala, amma dai, Allah da Ya aikata bazata a baya, zai iya maimaita hakan a wannan karon. A kasarnan ne muka ga gamayyar Jam’iyyu biyar suka tsayar da dan takara guda, Allah kuma Ya nu na ya fi su. Idan har za mu bar wa Allah komai, ya wajaba mu yi iyaka yin mu, kowa ya tabbata ya samu katin sa na zabe.”

Wawaye ne kawai ke gudu daga bakin daga. Yanda muka faro haka, ba zan taba zamewa na bar ku ba, ina nan tare da ku komai rintsi.

“Ku fa sani, za su yi maku barazana kala daban-daban, amma ka da ku karaya. Wawaye ne kawai ke karaya su juya baya a fagen daga. Yanda muka tako haka,ba zan taba yin watsi da ku ba. Kowa ya tanadi katin sa na zabe, ba na jin wani zai yi tunanin sake yi mani wata barazana. Ku fa tuna, na shiga kurkuku a kan laifin da ban san komai a kan sa ba,” in ji Obasanjo.

Shugaban tafiyar ta, ‘CNM,’ ya jaddada cewa, an kafa kungiyar ce domin ta ceci Nijeriya, daga halin kanikayin da take ciki yanzun, bayan tattaunawa sosai a kan hanyar da ya kamata a bi, ya ce a wannan karon mun dauko hanyar da za ta fisshe mu.”

“ba na jin a shekarun da nake da su yanzun, zan iya ci gaba da yin korafi ba tare da lalubo mafita ba. Na fada cikin jawabi na na ranar 3 ga watan Janairu cewa, an kafa wannann tafiya ta CNM ne domin ta fuskanci matsalolin Nijeriya sosai, da nufin samar da mafita. CNM ne za ta samo mana mafita daga halin da muka tsinci kanmu a halin yanzun.”

“In kuwa har za a samu wanda ke jin a ci gaba da yanda ake a halin yanzun, to ya kamata a binciki lafiyar kwakwalwarsa. Duk masu dandana kudarsu yanzun a Nijeriya, sannan kuma su na son a ci gaba a haka, tabbas makiya Nijeriya ne su.”

Ya kuma bayyana cewa, idan lokaci ya yi, kungiyar na su za ta shiga kawance da wasu kungiyoyin masu mahanga irin na ta. Ya kuma bukaci shugabannin kungiyar a dukkanin Jihohin kasarnan da su baiwa mata kashi 30, da kuma matasa su ma kashi 30 na dukkanin mukaman kungiyar.

A jawabin sa na maraba, Shugaban kungiyar na Jihar ta Oyo, Olaiwola Olakojo, ya yi nu ni da cewa, Obasanjo, shugaba ne da ya kamata a saurara ma ta kowane fanni. Obasanjo, mutum ne mai son ci gaban Dimokuradiyya da kuma Nijeriya a matsayin ta na kasa daya cikin zuciyar sa har a wajen ta.

“Obasanjo ne macecinmu. Ku lura da dukkanin ayyukan da ya yi a cikin gwamnatocin duniya da na nan cikin gida. Tabbas shi uba ne ga Nijeriya. A matsayin sa na shugaban dattawan kasarnan, a kullum fatan alheri ne yake yi wa Nijeriya. Maganganun sa da tsokacin shi a gwamnatocin jiya da yau, duk don neman ci gaban kasarnan ne,” in ji Olakoja, wanda tsohon Sakataren gwamnatin Jihar Oyo ne.

Wasu daga cikin jiga-jigan Jihar ta Oyo da suka halarci wajen sun hada da, Olagunsoye Oyinlola, Taofeek Arapaja, Oyewole Fasawe da Hammed Raji, da dai sauran su.


Advertisement
Click to comment

labarai