Connect with us

LABARAI

2018 Ce Shekarar Kammala Ayyukan Gwamnatin Ganduje –Kwamishinan Yada Labarai

Published

on


An bayyana kyakkyawan zaton da akewa Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na samun nasarar Kammala manyan ayyukan da ta faro da kuma wadanda ta gada tun zuwan ta kan karagar mulki, wannan bayani ya fito daga bakin Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Kwamared Muhammad Garba alokacin kaddamar da shirin sabunta bututun ruwa na shekara ta 2018, Kwamared Muhammad Garba yace a shekara ta 2017 Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta gina hanyoyin da suka tasamma dubunnan miliyan Naira kamar yadda ta alkawartawa Kanawa alokacin yakin neman zabe.

A cewar sa Gwamnatin Ganduje ta samu nasarar sauke amanar zakulo hanyoyin samar da kudaden aiwatar da muhimman ayyuka, samar da kayan more rayuwa, inganta harkokin ilimin bai daya (UBE). Kwamared Muhammad Garba ya ci gaba da cewa gwamnatin Ganduje ta yiwa kasafin kudin shekara ta 2018 kyakkyawan tanadi domin daukar matakin da ya kamata wajen kaucewa dogaro da kason da gwamnatin tarayya ke rabawa jihohi.

Saboda haka kasafin kudin da Gwamna Ganduje ya gabatarwa majalisar dokokin Jihar Kano, kasafin kudi ne da aka shirya domin tabbatar da karasa ayyukan tashar wutar lantarki mai zaman kanta mallakar gwamnatin Jihar Kano, sai kuma shirin gwamnatin Kano na kafa wata cibiyar horar da sana’un hannu domin dogaro da kai.

A kokarin Gwamna Ganduje na inganta harkokin ilimi tun zuwan wannan Gwamnati, Gogarman yiwa Jihar Kano kwaskwarimar da ta dace, Gwamna Ganduje ya tabbatar da ganin duk wani lissafin abubuwan da sashin ilimi ke bukata bai gamu da kowane irin tasgaro ba, musamman ga dalibai ‘yan salin Jihar Kano da ke karatu a Jami’o’i daban daban na kasashen waje, duk kuwa da matsalar tattalin arziki da aka fuskanta. Kwamaren Muhammad Garba ya ci gaba da cewa Gwamnatin Ganduje ta gaji tarin basuka wanda aka gadar mata na daliban dake karatu a kasashen waje.

Kwamishina Muhammad Garba ya kuma bayyana halin da gwamntin da ta gabata ta bar Jihar Kano a ciki ta fuskar tattalin arziki, ya ce gaskiyar al’amari shi ne kumajin da waccan gwamnati tayi-tayi na cewar ta biya kudaden karatun wadancan dlaibai ‘yan asalin Jihar Kano ba gaskiya ba ne, ya ce bayan gudanar da dogon bincike mun iske Gwamnatin da ta gabata ta yi amfani da wasu kwararru ne wadanda suka kitsa kitumurmurarsu kawai domin biyan bukatun wadanda suka kawo su.


Advertisement
Click to comment

labarai