Connect with us

LABARAI

Zazzabin Maleriya: Mutum Dubu Dari Uku Ke Mutuwa A Nijeriya -Kadala

Published

on


An bayyana mutum sama da mutum 300,000 ke mutuwa duk shekara sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro (Maleriya) a Nijeriya, shugaban shirin yaki da zazzaben cizon sauro a jihar Adamawa, Mista Isaac Kadala, ya bayyana haka a Yola babban birnin jihar.

Kadala ya yi bayanin cewa, gwamnatin jihar Adamawa ta samar da magunguna da gidajen sauro, kayayyakin gwaji da kuma yiwa jama’a jinyar kwayar cutar kyauta.

Shugaban ya shawarci jama’a da’a kowani lokaci su rika zuwa ana musu gwaji, domin magance duk wata zazzabe da’ake tsammanin maleriya ce, yace yin haka shi zai basu tabbacin basu dauke da kwayar cutar maleriya

A na bangaren kuma gwamnatin jihar Adamawa ta ce ta ware naira miliyan dubu biyu domin yakar cutar zazzaben cizon sauro (malaria), a jihar nan da shekarar 2020.

Da take magana game da makon zazzaben maleriya kwamishiniyar lafiya ta jihar Dakta Fatima Atiku Abubakar, tace gwamnatin jihar ta dauki matakan da ya dace domin kawo karshen annobar zazzaben a jihar.

Ta ci gaba da cewa gwamnatin jihar ta ware zunzurutin kudi naira biliyan biyu, domin yaki da cutar zazzaben cikin shekarun a jihar baki daya.

Dakta Fatima Abubakar, wacce babban sakataren ma’aikatar Mista Kennedy Bartimawus, ya wakilta yace daga cikin watan Nuwanban 2017, gwamnatin jihar ta raba gidajen sauro kimanin miliyan biyu da dubu dari biyar, domin yakar cutar.

“manufarmu shine akalla kowani gida muna son su samu gidan sauro guda daya, domin su rabu da cizon sauro a kowace dare” inji Dakta Fatima.

Kwaminiyar ta kara da cewa gwamnatin jihar kan yiwa mutane gwajin zazzaben maleriya kafin ta baiwa kowani mutum magani, tace idan kuma aka samu mutum dauke da cutar ana bashi kyakyawar kula da magunguna.


Advertisement
Click to comment

labarai