Connect with us

LABARAI

Ya Wajaba Buhari Ya Duba Matsalolin Mata Da Matasa A Nijeriya –Uba Boris

Published

on


A daidai lokacin da shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya kammala ziyarar aiki a Jihar Bauchi domin kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin Mohammed Abdullahi Abubakar da gwamnatin tarayya suka aiwatar, an shawarci shugaban kasa Buhari da ya waiga baya ya duba irin kokarin da mata da matasa suka yi wajen kawo gwamnatin sa a karkashin tutar jam’iyyar APC ta hanyar kara himmar samar musu da ayyukan yi don a daina amfani da su wajen aikata ayyukan da ba su dace ba a cikin al’umma.

Alhaji Uba Boris dan siyasa a Jihar Bauchi kuma mai rajin kare hakkokin mata da matasa shi ne ya bayyana haka cikin hirar sa da wakilin mu game da wannan ziyara da shugaban kasa Buhari ya kawo Jihar Bauchi, inda ya yi fatar ziyarar za ta haifar da alheri a tsakanin jama’ar Jihar Bauchi tare da bayar da abubuwan daka aka yi alkawari don inganta rayuwa.

Game da karancin aiki da ake cewa jihar Bauchi na fiskanta daga wannan gwamnati saboda ba wani aikin azo a gani da gwamnatin Bauchi ta yi wanda shugaban zai kaddamar illa na gwamnatin tarayya wanda suka shafi hanyoyi da barakin sojan sama da shugaba Buhari ya bude, Alhaji Uba Boris ya bayyana cewa wannan magana siyasa ce saboda duk abin da za a bude an gani a kasa ya ke kuma mutane sun gani an bude duk abin da aka fada don haka ya kamata mutane su fadi alheri.

Don haka ya ce ba za a hana kowa ya fadi maganar sa ba, amma ya kamata mutane su rika fadin gaskiya da yi wa gwamnati adalci da uzuri su kuma bayyana abin da zai taimaki kasa da Jihar Bauchi da al’umma ba abin da zai haifarda matsala a cikin kasa ko kiyayya ga shugabanni ba.

Alhaji Uba Boris game da halin da mata da matasa ke ciki ya roki shugaban kasa Buhari ya duba halin da suke ciki na rashin aikin yi musamman ganin matasa da mata su ne suka taka rawar gani wajen kawo wannan gwamnati kuma suna neman tallafi a wannan lokaci don su samu abin yi, don haka ya roki shugaba Buhari ya tallafi matasa da mata a kasa baki daya don su samu abin yi mai dorewa ta hanyar samar da masana’antu da ayyukan ofis da za su farfado da wuraren da suka mace a sassan kasar nan.

Ya ce, idan mutane suka samu abin yi duk irin rigingimun da ake fama da su a cikin kasar nan dole za su ragu. Amma rashin abin yi da zaman kashe wando da mata da matasa ke yi yawanci shi ne ke haifar da matsalolin tsaro ta yadda bata gari ke amfani da matasa wajen aikata miyagun ayyuka.

Don haka ya zamo wajibi a daidai wannan lokaci a waiwaya a duba matasa game da irin halin da suke ciki na rashin abin yi a duk Nijeriya, don matukar aka ci gaba da kallon su suna zaune kara zube to akwai matsala idan aka fara gangamin siyasa za a rika amfani da su wajen aikata abin da bai dace ba don biyan bukatun wasu kalilan mutane musamman ‘yan siyasa.

Amma idan har suna da ayyukan yi zai kasance suna tsoron sanya kawunan su cikin wata hidima da za ta haifar musu da matsala a rayuwa ko kaiwa ga sallamar su daga aikin da suka san mai dorewa ne.

 


Advertisement
Click to comment

labarai