Connect with us

LABARAI

Za Mu Kara Matakan Tsaro A Jihar Katsina

Published

on


Sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina Muhammad wakili ya bayyana cewa zai canza salon tsaro a jihar Katsina domin neman nasarar dakile miyagun ayyuka a dukkan fadin  jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya zo karamar hukumar Malumfashi da Kafur a ci gaba da ziyarar da yake yi a kananan hukumomin jihar.

Kwamishinan ya fara tsayawa ne a karamar hukumar Malumfashi kuma Kwamandan Shiyyar ta Malumfashi ne ya karbi bakuncin kwamishinan, daga nan sai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan D.S.P Garba Isah ya gabatar da shi ga mutanen  da suka samu halartar wannan taro. Sannan ya ci gaba da fadin dalilinsa na yin wannan rangadinn. Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewar yazo karamar hukumar Malumfashi da Kafur ne domin ya gaya wa masu ruwa da tsaki a kan harkokin tsaro na wannan shiyyar kamar yansanda masu sa kaki da ‘yan sanda ciki da sebil Depence jami’an tsaro na farin kaya da sojoji da kwastam da imagireshan da ‘yan sintire da sauran makamantansu game da kalubale na harkar tsaron jihar katsina. Kwamishinan ya kara da cewar wajibinsu ne su mike tsaye domin kara kaimin tsaro a wanan shiyyar da jihar Katsina baki daya. Uban kasa Galadiman Katsina Hakimin malumfashi Hon Jostis Mamman Nasir a bayaninsa na maraba da manyan baki ya nuna farin cikinsa ne game da wannan ziyara da kwamishinan ya kawo  Malumfashi da Kafur.

Sannan kuma ya umurci al’ummar wannan yanki su ci gaba da ba ‘yan sanda hadin kai da goyon baya game da aikinsu na kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu, sannan aka zarce karamar hukumar Kafur wanda a nan ma D.S.P Garba Isah ya gabatar da kwamishinan ‘yan sandan ga dimmbin jama’ar da suka halarci wannan taro sannan kwamishinan ,ya ci gaba da bayaninsa kamar yadda ya gabatar a Malumfashi kuma ya kara da cewar suna bukatar addu’a domin sha’anin tsaro sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi a jihar Katsina .

A na sa jawabin a wajen taron Uban kasa Dangaladiman Katsina hakimin Kafur Alhaji  Rabe ya nuna farin cikinsa game da bayanin  kwamishinan na kara kaimin tsaro a duk fadin jihar sannan ya umarci jama’a su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai da goyon baya domin samun nasarar aikin su. Magajin garin Kafur Alhaji Abdulkarimu Umar shi ma ya yi mtsokaci a wurin taron ida ya ce jama’ar Kafur su ci gaba da biyayya ga shugabanni domin an ce bin na gaba bin Allah.

 


Advertisement
Click to comment

labarai