Connect with us

LABARAI

Mai Wa Kasa Hidima Ta Mutu A Sansanin NYSC Da Ke Kwara

Published

on


Daya daga cikin mata ‘yan yi wa kasa (NYSC), mai suna Miss Hilda Eba Amadi ta gamu da ajalinta a sakamakon raunuka da ta samu a lokacin da suke tsaka da gudanar da horon wanda ake ci gaba da yi a sansanin ‘yan yi wa kasa hidima da ke Yikpata wanda ke karamar hukumar Edu a jihar ta Kwara.

Mi yi wa kasa hidimar da ta gamu da ajalinta, wacce ta samu shaidar kammala karatun Digiri a jami’ar Fatakwal, inda kuma ta karanci ilimin Mai da Iskar Gas, rahotonin sun zo kan cewar lafitar kalau ta shiga hidimar aikin Bauta wa kasa na shekara guda a wannan jihar ta Kwara.

An rawaito cewar marigayiyar ta fado ne daga kan wata na’ura wanda jami’an kungiyar sa kai ta ‘Man O War’ suka kafa a farfajiyar sansanin nazarin sanin makamar aiki ta NYSC din.

Wata majiya da ta nemi ‘yan jarida da su suturceta, majiyar kuma daga sassanin, majiyar ta shaida wa ‘yan jarida a garin Ilorin, tsautsayin ta faru ne a tun lokacin da ta fado kasa rigijim, inda aka yi kokarin garzayawa da ita zuwa karamin asibitin jinya da ke cikin sansanin  ta NYSC domin kulawar likitoci.

Majiyar sun yi bayanin cewar dalibar da ke neman sanin makamar aikin ba ta samu kulawar kwararrun likitoci ba, a wannan asibitin sansanin a lokacin da take matsanancin bukatar agajin gaggawa.

Sun ci gaba da bayyana cewar a lokacin da aka yi kokarin garzayawa da ita babban asibitin Ilorin domin kara samar mata da kulawar manyan likitoci ne kuma sai rai ya ce ga garinku, inda ta mutu a wannan yanayin.

Haka zalika, wasu daga cikin abokan amsar horon marigayiyar da suka bayyana alheninsu kan rasuwar a jiya Juma’a, sun shaida wa manema labaru cewar hakan ta faru ne a sakamakon nuna halin ko-in kula daga hukumar ta NYSC.

Kamar yadda suka shaida, “Hukumar gudanarwa ta NYSC sun gaza samar da nagartattun kuma kwararrun ma’aikatan jinya da za su kula da mambobin da suke samun horo a wannan sansanin,” In ji su.

A lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na NYSC, Mr. Oladipo Morakinyo domin samun tabbacin mutuwar ‘yar yi wa kasa hidimar, ya bayyana cewar kawo yanzu yana kan tattaro muhimman bayanai domin samar da sahihin bayani kan lamarin.

 


Advertisement
Click to comment

labarai