Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Kaduna Ta Horas Da Matasa 540 Sana’o’i

Published

on


A koakarin da take yi na samarwa matasa aikin yi a dukkan fadin jihar. gwamnatin jihar Kaduna ta haras da matasa guda 540 sana’o’i daban-daban, wadanda Cibiyar koyar da sana’a’i ga al’umma tab a su horon.

Su dai wadannan matasa sun fito ne daga karamar hukumar Kaura da Sabongari da Igabi.

Kwamishina a ma’aikata kasuwanci, Masana’antu da yawon bude ido Misis Ruth Alkhali c eta bayyan haka, sannan kuma ta ce, dukkan wadanda suka amfana da wannan horaswas matasa ne wadanda shekarunsu suka kama daga 18 zuwa 24 wadanda kuma suka kunshi daliban da suka gama makaranta da almajirai da yara marasa galihu da kuam matasan da ke da nakasa.

Ta ce wannan hoaraswar da aka yi wa matasan an yi ta ne bisa hadin gwiwar wani shiri na musamman mai suna Mafita, DFID  da kuma gwamnatin jihar Kaduna. Saboda haka dukkan matasan da suka samu wannan horo za su samu sauki wajen tafiyar da rayuwarsu domin kuwa sun samu hanyar dogaro da kansu wada kuma har sauran al’umma za iya taimakawa ko ma su taimaki kasa baki daya.

Ta ce tun bayan da aka gyara Cibiyar koyar da sana’ao’in kuma ta samu tallafin  cikakakkun kayan aiki, take koyar da matasa hanyoyin dogaro da kai, saboda haka yanzu haka an samu gagarumin ci gaba a wanna Cibiya..

Daga cikin sana’o;in da aka koyar da matasan akwai dinkin manyan riguna da aikinmkafinta da kera kayan karau na mata da aikin wutar lantarki  da walda da sauran sana’o’i daban-daban.

Haka kuma kwamishinar ta ce wannan horaswas an yi ta ne daidai da yadda makarantun koyar da sana’o’i na gwamnati ke yi.

Kamar yadda ta ce akwai koyar da karatu da rubutu da ake yi a cikin aji sannan kuma akwai kuma aikata abin da aka karanta , domin a tabbatar da yadda yake amfani.

haka kuma an koya wa matasan sana’o’i daban-daban na tsawon wata tara, wanda salon koyarwar da aka yi musu sai da aka tabbatar dacewa sun iya abin da ake kokarin koyar da su.Koma kamar yadda ta ce kwalliya ta biya kudin sabulu.

Tun da farko ana nasa jawabin gwamna jihar Kaduna Malam Nasiru El-wanda mataimakinsa Barnabas Bala Banted ya wakilta ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da fadada wanna shiri yadda matasa daga kowace karamar hukuma afadin jnihar Kaduna  za su amfana da wannan horaswa.

Saboda haka sai ya tabbtar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba wannan Cibiya cikakken goyon baya, yadda za ta ci gaba da samun nasarar aiwatar da ayyukanta.

A karshe kuma sai ya yi kira ga masu hannu da shuni kan su kawo wa wannan Cibiya gudummawa, domin taimakawa matasan jihar Kaduna wajen samar musu da aikin yi.


Advertisement
Click to comment

labarai