Connect with us

LABARAI

Dangote zai Gina Masana’antar Sarrafa Tumatur Da Shinkafa

Published

on


Hamshakin attajiri kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana aniyarsa ta kashe miliyoyin Dala wajen gina masana’antar sarrafa tumatur da shinkafa a jihar Katsina.

Attajirin ya bayyana hakan ne lokacin da suke zantawa da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari a gidan Muhammadu Buhari da ke Katsina, wanda kuma ya tabbatarwa da gwamnan cewa nan da ‘yan makwanni kadan masu zuwa za a fara aikin gina kamnonin.

Dangoten ya ci gaba da cewa, baya ga kafa wadannan kamfanoni, za kuma tallafawa manonma yadda za su samu damar noma a bin da za sarrafa a wadannan masana’antu.

“Za mu ci gaba da bayar da gudummawarmu wajen bunkasa noma. za mu hada kai da gwamnati wajen ganin an taimaki manoma a kasar nan yadda za su ci moriyar sana’ar ta su ta noma kamar yadda ya kamata, na kuma zo nan da kaina ne domin in nuna muhammanci da na dauki bunkasa harkar naoman da shi’.

“Na san mun sha yin huldodi da wannan gwamnati a kan abubuwa daban-daban, amma wannan karon na zo da kaina ba sako ba, domin in nuna wa gwamna tare da tabbatar masa da aniyar da nake da ita na kafa wadannan masana’antu tare da tallafawa manoman wanna jiha” In ji shi.

Saboda haka, sai ya bukacin al’ummar wannann jiha da su tabbatar sun ci moriyar wadannan masana’antu kamar yadda ya kamata, sannan kuma ya kara tabbatar da cewa bayan wadannan ma akwai shirin sake kafa wadansu masana’antun da yake yi a wannan jihar

 


Advertisement
Click to comment

labarai