Connect with us

LABARAI

An Karya Lagon APC A Jihar Nasarawa – Hon Sani

Published

on


Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarwa ta yi ikirarin cewa kawo yanzu ta karya lagon abokiyar adawarta mai mulki a jihar, wato APC, ta yadda ba za ta iya yin wani tasiri ba a zabubbuka masu zuwa duba da yadda ‘ya’yan PDP masu rike da mukamai daban-daban kuma a matakai mabambanta ke ta kokarin inganta rayuwar jama’ar yankunansu domin shayar da su romon dimokuradiyya.

Wadannan bayanai sun fito ne daga bakin Honarabul Sani Mohammad Keffi wanda shi ne shugaban matasan PDP na Jihar Nasarawa, sa’ilin da yake jawabi a wajen taron raba tallafin motoci guda 32 ga Jam’iyyarsu ta PDP wanda dan majalisar wakilai Honarabul Gaza Jonathan Gbefwi ya yi ya kuma gudana a karamar hukumar Karu a Juma’ar makon jiya.

A wannan rana ce Hon. Gaza mai wakiltar yankin Karu/Keffi/Kokona daga Jihar Nasarawa a majalisar wakilai ta kasa ya yi rangadi tare da kaddamar da wasu ayyukan cigaban al’umma a mazabarsa don amfanin jama’arsa.

A tashin farko dai dan majalisar tare da tawagarsa sun ziyarci kauyen Amba da ke yankin karamar hukumar Kokona inda ya kaddamar da aikin gyaran hanya domin saukake wa al’ummar yankin sha’anin zirga-zirga da ababen hawa da kuma samun saukin fitar da amfanin gona da sukan noma zuwa wasu sassa.

Bayan haka, Hon Gaza ya yada zango a karamar hukumar Karu inda a nan ya raba kyautar kananan motoci kirar ‘Golf’ har guda 32 ga daukacin ofishin jam’iyyarsu ta PDP da ke unguwanni 32 a fadin shiyyar da yake wakilta a majalisar wakilai ta kasa. Inda karamar hukumar Karu ta samu motoci 11, Kokona 11, sai kuma Keffi da ta samu motoci 10.

Da yake bayani game da wadannan ayyukan cigaba da ya aiwatar, Hon Gaza ya ce ya yi haka ne domin inganta rayuwar jama’ar mazabarsa tare da ba su tabbacin cewa ba su yi zaben tumun dare ba. Ya kara da cewa, wadannan ayyuka kadan ne daga cikin ribar dimokuradiyya da yake da zummar samar wa yankin nasu.

Baya ga aikin gyaran hanya da dan majalisar ya kaddamar a Amba, haka ma akwai aikin samar wa kauyen wutar lantarki wanda tuni aikin ya yi nisa duka dai a karkashin daukar nauyinsa.

Game da motocin da ya raba, Hon. Gaza ya ce ya yi haka ne domin samun damar ci gaba da yi wa jam’iyyarsu ta PDP hidima yadda ya kamata. Ya kara da cewa, motocin za su zauna ne a karkashin kulawar ciyamomi na PDP na unguwanni da ake da su. Ga baki daya, wadanda ayyukan dan majalisar suka shafa sun nuna godiyarsu tare da bai wa dan majalisar tabbacin cewa suna tare da shi duk inda ya shiga.

Da yake tofa albarkacin bakinsa game da ayyukan dan majalisar, shugaban PDP na Jihar Nasarawa Mr. Francis Orogu, ya yaba da kokarin dan majalisar, tare da cewa Hon. Gaza ya aikata abin da babu wani dan siyasa da ya taba aikata kwatankwacinsa a fadin Jihar Nasarawa. Sannan ya yi kira ga jama’a da a basu cikakken goyon baya yayin zabubbuka masu zuwa.

Taron ya kammala lami lafiya tare da samun mahalarta da dama daga sassa daban-daban, ciki har da mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewa ta tsakiya Hon. Theophilus Dakas Shan da shugaban PDP na jihar Nasarawa Mr. Francis Orogu da dan takaran sanata a jihar Hon. Aliyu Bala Ahmad Tafida (Matawallen Nasarawa) da dai sauransu..

 


Advertisement
Click to comment

labarai