Connect with us

LABARAI

Zan Dauki ’Yan Sanda Miliyan Biyu Idan Na Ci Zabe –Moghalu

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

Tsohon mataimakin babban Bankin Nijeriya, Farfesa Kingsley Muoghalu, ya sha alwashin daukan sabbin ‘yan sanda milyan biyu aiki domin su kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya, da zaran an zabe shi a matsayin shugaban kasannan a watan Mayu 2019.

Ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Abeokuta, ta Jihar Ogun, bayan kammala wani taron zama da al’umma mai taken, “The Role of Youths and Women in Good Gobernance”.

Moghalu, ya yi nu ni da cewa, Jami’an tsaron na ‘yan sanda sun yi wa kasarnan kadan bisa la’akari da yawan al’ummanta da kuma ‘yan sanda da ake da su a yanzun haka.

Ya kuma bayyana cewa, daukan sabbin ‘yan sandan zai rage yawan dimbin karfafan matasan mu da ba su da aikin yi.

“In ba tatsuniya ba, ta ya za a ce kasar da ke da yawan mutane milyan 200, sai kuma a ce wai kwata-kwata,’yan sandan ta 300,000 ne kacal? Ai wannan wasan yara ne.

“Sam ba tsaro a kasarnan. Don haka za mu dauki sabbin ‘yan sanda milyan biyu, hakan kuma wata dama ce ta kara samar da aikin yi ga milyoyin ‘yan Nijeriya. Za mu dauke su mu kuma ba su horo ingantacce mu kuma wadata su da dukkanin kayan aikin da ya kamata.

Ya kuma bayyana hanyoyin da gwamnatin Shugaba Buhari ke tutiyan ta samar wa matasan na rage talauci da cewa, duk buge ne kawai, hanyoyi ne ma da za su kara dankwafar da matasan cikin talauci.

“Ta ya za a ce kana baiwa mutane Naira 5000, sannan ka ce wai kana kawar ma su da talauci, wannan ai kana kara cusa su a cikin talaucin ne,” in ji Moghalu.

“Don Allah, me Naira 5000 za ta yi wa mutum mara aikin yi? Ba abin da za ta tsinana ma shi! Ai ko ba shi da iyali, cikin kwanaki biyu 5000 za ta kare! Sam ni na bambanta da wannan, ni manufa ta ita ce, ta ya zan  azurta ‘yan Nijeriya, ta ya zan  sama wa ‘yan Nijeriya ayyukan yi. Ni tunani na daban ne, ina da dubarun yin hakan,na kuma san ina da hikimar tsarawa da aiwatar da hakan.”


Advertisement
Click to comment

labarai