Connect with us

LABARAI

Zaben Kananan Hukumomi Na Nan Daram A Kaduna –Hukumar Zabe

Published

on


Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

An bayyana cewa zaben Kananan Hukumomi dake tafe a fadin Jihar kaduna, na nan daram babu gudu ba ja da baya, duk da kalubalen da hukumar zaben ke fuskanta na gobarar da ya tashi a ofishin hukumar a makon jiya.  Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Dakta  Saratu Binta Dikko, Shugabar Hukumar Zaben Jihar Kaduna, wanda a turance ake kira da Siecon.

Shugaban hukumar zaben, Saratu Binta Dikko ta bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da aka yi da masu ruwa da tsaki da kuma Shugabanin jam’iyyu, da masu lura da harkar zabe a Jihar Kaduna.

Ta ce Babu maganar dage ranar zaben Kananan Hukumomin da aka sanya zai guda a ranar  12 ga watan Mayu mai zuwa.

Ta kara da bayyana cewa,  “Zamu yi dukkan mai yuwuwa domin tabbatar da adalci, saboda Dimokuradiyya shi ne aiwatar da zabe tare da bayar da sakamakon nasara ga duk wanda ya yi nasara”.

Shugaban hukumar zaben, ta kara da cewa, “duk da mun dan sami ibtala’i na gobarar da ya tashi a wani sashen ofishinmu, amma hakan ba zai hanamu gudanar da zabe kamar yadda muka ayyana a baya ba. Sannan ina kira ga masu cewa wai da wuya mu sami damar gudanar da wannan zabe da ya zo mana a kurarren lokaci, wannan ba gaskiya ba ne, domin babu wani rana daya da muka taba yunkurin daga wannan zabe da muka kudiri aniyar gudanar da shi a ranar 12 ga watan mayu, idan Allah ya kaimu.”

Dangane da maganar da ake yi na cewa ko za’a gudanar da zaben ne da komfuta, kamar yadda hukumar tayi alkawari a can baya. Shugaban hukumar zaben ta bayyana cewa, da wuya zaben ya iya gudana da komfuta kamar yadda aka tsara gudanarwa, saboda a cewarta, rashin amincewar hakan ya biyo bayan kin amincewa da hukumar zaben ta kasa wato INEC, tayi na kin amincewa ayi amfani da mashinan zaben na komfuta, saboda abin da hukumar ta kira, shirye shiryen da take gudanarwa na fuskantar zabukan shekara ta 2019 mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Wadanda suka sami halartar taron sun hada da jami’an tsaro, ‘Yan siyasa, ‘Yan jarida da duk wasu masu jibi da batun zaben,  domin ganin an  tafi tare domin samun  gudanar da zaben Kananan Hukumomi  kamar yadda ya dace.

Duk da wasu da yawa daga cikin mahalarta taron sun nuna gamsuwar su da taron da abin da aka tattauna. Amma a bangare daya kuma, wasu Shugabanin Jam’iyyu sun nuna kin amincewarsu da wannan zabe, kamar yadda Sakataren jam’iyyar APC ya bayyana na cewar, sun rubutawa hukumar zaben takardar korafin cewa, zaben Kananan Hukumomi, yazo dai dai da ranakun gudanar da zabukan Shugabani da Mambobin jam’iyyar APC da za’a gudanar a fadin kasar nan baki daya.


Advertisement
Click to comment

labarai