Connect with us

LABARAI

Yadda Sinawa Suka Zuba Tsagwaron Basira A Tashar Tekun Yangshan

Published

on


A sakamakon muhimmancin da tashar taku ta ke da ita wajen bunkasa tattalin arzikin ko wace kasa a duniya, Kasar Sin ta muhimmanta samar da tashoshin teku da suka dace da hada-hadar zamani domin kara bude kofofin arziki ga al’ummarta.

A kan wannan kudiri ne Sinawa suka gina wata tashar teku mai zurfi ta Yangshan inda suka nuna tsagwaron basirar da suke da ita a kan kirkira da aiwatarwa.

Tashar ta Yangshan an gina ta ce a arewa-maso-gabashin yankin Hangzhou Bay a tekun Kiku Archipelago da ke arewa-maso-yammacin takwararta ta tashar tekun Luchao a Birnin Shanghai, birni mafi girman hada-hadar kasuwanci a Kasar Sin.

Tashar an sada ta da hanyar motoci ta kan tudu bisa amfani da kwarewa wajen gina gadar da ta tsaga tekun mai nisan kilomita 32. Tashar tana mokataka da kogin Yangtze da ke da tazarar kilomita 72 a tsakaninsu da kuma tashar teku ta Ningbo ta yankin kudanci wanda tsakaninsu akwai nisan kilomita 90, kana da hanyar fiton kaya ta ruwa ta kusurwar gabas da ke da tazarar kilomita 104.

An gina tashar teku ta Yangshan ta yadda za ta zama cibiyar hada-hadar kasuwancin dakon jiragen ruwa ta duniya a kan manyan hanyoyin fiton kaya ta ruwa da ta sada yankin Asiya da Amurka da kuma wacce ta sada Asiya da Kasashen Turai.

Baya ga zama wani mataki mai muhimmanci ga cigabanta, har ila yau samar da tashar ta Yangashan wani babban jigo ne ga cimma nasarar gina Babbar Cibiyar Fiton Kaya ta Ruwa ta Duniya a Birnin Shanghai. An fara gudanar da aikin gina tashar ta Yangshan a shekarar 2002 inda a tsakanin shekara shida da rabi aka kammala kashi na daya da na biyu da na uku. Tashar tana da katafaran wuraren sauke kayan da manyan jiragen ruwa suka yi dako daban-daban guda 16 ta kudancin yankin Diaoyangshan. A sakamakon kara fadada yadda za a ci gajiyar tashar sosai, sannu a hankali burin Kasar Sin zai cika a kan mayar da tashar babbar cibiyar da za ta janyo hankulan kasashen duniya a kan hada-hadarsu ta teku.

An tsara tashar tekun Yangshan zuwa sassa hudu, akwai tazarar tsawon mita 5.6 a tsakanin na daya da na biyu da na uku inda sashe na hudu yake da tazarar tsawon mita 500 a tsakaninsa na uku. Duka sassan; hada-hada ta kankama a cikinsu sai dai sauran sun riga sashe na hudu farawa, da yake shi a bara ne amfani da shi ya kankama.

A halin yanzu tashar tekun  Yangshan ta zama mafi girman hada-hada a duniya inda ta daram ma ta Singafo da ta ke rike da kambin a duniya da shige da ficen manyan sundukan kaya sama da milyan 40. Baya ga sashen sauke manyan sundukan kaya, har ila yau akwai wani gefe da aka ware a tashar domin sauke mai da gas da Kasar Sin ta ke sayowa daga Kasar Maleshiya.

 

Wakazalika, duk da Kasar Sin ta samu tashar tekun da babu irin ta a duniya a halin yanzu, tana kuma da burin gina wata tashar duk dai a tekun mai zurfi ta Shanghai da za ta fi tashar Yangshan girma. Za a gina gadar da za ta keta tekun ta sada tashar da kan tudu mai nisan kilomita 40. Baya ga hanyar motoci, har ila yau za a gina layin dogo shi ma da zai keta tekun ya sada tashar da kan tudu.

Da yake wa tawagarmu karin haske game da tashar tekun ta Yangshan, Daraktan Kamfanin Shanghai Tongsheng Inbestment Group Company Ltd da ke kula da tashar, Mista Du Wei, ya bayyana cewa fiye da kamfanonin aikin injiniya 20 suka yi aikin gina tashar wadda ya ci kudi kimanin dalar Amurka bilyan 12.

Ya ce tashar tana da ma’aikata sama da 17,000 amma wadanda suke aiki a kwaryar tashar mutum 2000 ne.

Da aka tambaye shi irin kalubalen da suka fuskanta wajen gina tashar ta Yangshan, Daraktan ya ce abu na farko shi ne samar da tsibirin da za a gina tashar. Domin a cewarsa, wurin da aka gina tashar a lokacin da za su fara aiki bai wuce da kashi 10 a cikin dari ba, sauran kashi 90 a cikin dari kuma su ne suka samar a cikin ruwa suka hada da ragowar da suka tarar wadda ya ce shi ma sai da suka yi aikin gyara kafin ya amfanar yadda suke so. Haka nan ya ce, kafa na’urorin aikin gina tashar a cikin tsakiyar ruwa ba abu ne mai sauki ba saboda wurin da aka zaba don gina tashar ya fi ko ina zurfin ruwa a cikin tekun.

Mista Du Wei, ya kuma ce har aka yi aikin aka kammala ba a samu asarar ran mutum ko daya ba, sai dai raunukan da wasu ma’aikata suka samu. A cewarsa, an samu nasarar hakan ne sakamakon yadda aka muhimmanta kula da lafiyar ma’aikatan da ke aikin fiye da aikin kansa, domin an yi tanadin kwararrun jami’ai na musamman masu kula da lafiyar ma’aikatan.

A tashar tekun ta Yangshan dai, baya ga ma’aikatan hana fasa-kwauri (kwastam), yana da matukar wahala a ga wani mutum yana kaiwa da komowa a tashar sakamakon yadda aka tsara yin komai da komai da na’ura. Hatta masu ba da damar sauke kaya ko yin lodi ba a ganin fuskar kowa a waje, daga cikin ofishinsu suke komai.

Da aka nausaya da tawagarmu zuwa wani dogon bene domin ganin yadda hada-hada ke gudana a cikin tashar, mun tarad da kaya da dama a wurin na kamfanonin kasashen duniya daban-daban wadanda aka sauke daga jirgi ko za a yi lodinsu.

A rahotanninmu na gaba za mu kawo cikakken bayani a kan gadar da ta sada tashar Yangshan da kan tudun Birnin Shanghai.

 


Advertisement
Click to comment

labarai