Connect with us

LABARAI

Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya Na Bauchi Ya Nemi Kungiyoyi Su Yi Koyi Da Ecowas

Published

on


Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Kwamandan kwamitin unguwanni domin samar da zaman lafiya a Jihar Bauchi Alhaji Isa Jibrin Makama ya shawarci kungiyoyi masu zaman kan su a Nijeriya kan su yi koyi da kungiyar inganta tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS domin wayar da kan jama’a game da fa’idar zaman lafiya tare da horas da mutane yadda za su rika isar da sakon zaman lafiya a cikin al’umma kamar yadda kungiyar ECOWAS ta aiwatar a Jihar Bauchi da wasu jihohin Nijeriya a kwanakin baya.

Jibril Isa Makama kwamandan ‘yan kwamiti na kato da gora ya bayyana cewa irin taron da kungiyar ECOWAS ta shirya ya kwanakin baya ya ilmantar da su muhimmanci da matsayin zaman lafiya a Nijeriya musamman ganin yadda aka samu zaman lafiya kimanin kashI hamsin cikin dari, don haka ya ja hankalin jama’a da suke halartar tarurruka don samar da zaman lafiya irin wanda ECOWAS ta shirya a Bauchi da cewa ya kamata kungiyoyin masu zaman kan su ya kasance sun yi koyi da irin wannan shiri don inganta zaman lafiya a Nijeriya.

Alhaji Isa Jibrin ya shawarci gwamnati kan ta himmatu wajen jajircewa kan lamarin tsaro ta hanyar tallafawa kungiyoyi masu zaman kan su da kwamitocin da suke taimakawa wajen inganta tsaro a Nijeriya don a samu sukunin gudanar da zabukan shekarar 2019 lafiya ba tare da samun matsala ba. Don haka ya kara da jawo hankalin mutanen da suke halartar tarurrukan da gwamnati ke shiryawa ko wanda kungiyoyi ke shiryawa kan zaman lafiya ya kamata mutane su rika isar da irin wadannan sakonni gaba don amfanin al’umma saboda an ce zaman lafiya ya fi zama dan sarki.

Don haka ya roki gwamnati a kowane mataki da su hamzarta tare da yin kokari wajen samar da ayyukan yi na zahiri ga matasa ba ayyukan jeka na yi ka ba, don hakan shi ne zai sa matasan su kasance sun natsu sun zama mutanen kirki. Har wa yau ya bayyana cewa samar da ayyukan yi  na zahiri za su tallafi jama’a tsayawa wuri guda domin neman abin kan su ba tare da sun shiga hanyoyi marasa kyau da za su taimaka wajen gurbacewar tarbiyyar su ba. Inda ya kara da cewa kudin da za a kasha wajen inganta tsaro da shiryar da mutane idan sun kauce hanya ya fi kudin da za a kashe wajen gyara musu rayuwa da samar da kayan more rayuwa wanda mutane za su yi farin ciki su rika sa albarka wa gwamnati.


Advertisement
Click to comment

labarai