Connect with us

LABARAI

Sauya Jadawalin Zabe: Kotu Ta Taka Wa Majalisa Birki

Published

on


Daga  Sulaiman Bala Idris, Abuja

A jiya ne Mai Shari’a Ahmed Mohammed na Babban Kotun Tarayya dake Abuja ya taka wa Majalisar Dattawan Nijeriya birki dangane da yunkurin da suka yi na sauya jadawalin zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Mai Shari’a Mohammed a hukuncin da ya yanke, ya bayyana cewa hukumar zabe mai zaman kanta INEC ce kadai ke da hakkin kawo sauye-sauye a jadawalin zabe a fadin tarayyar Nijeriya.

“Na aminda da zantukan masu kara akan cewa INEC ce kadai ke da ikon tsarawa tare da gudanar da zabe a fadin tarayyar kasar. A dalilin haka kuma, su ne ke da ikon shirya jadawalin zabe.” inji shi

Idan dai ba a manta ba Majalisar dattawa ta yi wani yunkuri a kwanakin baya domin gabatar da suaye-sauye ga jadawalin zaben shekarar 2019 da hukumar INEC ta fitar.

Sai dai kundin tsarin shekarar 1999 ya bayyana cewa Majalisar ba ta da hurumin yi wa INEC katsalandan akan sha’anin tsara jadawalin zabe.


Advertisement
Click to comment

labarai