Connect with us

LABARAI

Sarkin Musulmi Ya Bukaci A Rika Wayar Da Kai Kan Muhimmancin Zakka

Published

on


Daga Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga Hukumomi da Kwamitocin Zakka da Wakafi a fadin kasa bakidaya da su rika ilmantar da Musulmi masu hannu da shuni kan muhimmancin tallafawa mabukata.

LEADERSHIP A Yau ta labarto cewar Shugaban na Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin a yayin da ya karbi tawagar jami’an Hukumomin Zakka da Wakafi daga jihohi daban-daban a Sakkwato.

Mai Alfarma ya bayyana cewar bayar da Zakka wajibi ce a Musulunci wadda ke taimakawa wajen karfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin masu hali da marasa galihu a cikin al’umma.

“Don haka akwai bukatar mu wayar da kan Musulmi da karfafa masu guiwa kan bayar da Zakka domin samun nasarar kyakkyawan sakamako. A bayyane yake cewar za a rika yabawa da cewar jajircewar mu da sadaukar da kan mu domin samun nasara.”

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya kuma tabbatar da cewar zai ci-gaba da jajircewa domin samun nasarar bayar da Zakka ga al’umma daga nan ya kuma yabawa jami’an kan karfafa ayyukan Zakka da Wakafi a kasar nan.

Wakilin mu ya labarto cewar Sarkin Musulmi ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su rika taimakawa mabukata domin saukaka masu halin da suke ciki.

Tun da fari, Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi na Jihar Sakkwato, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewar wakilan taron sun zo Sakkwato ne domin gudanar da taron kwanaki biyu kan Zakka da Wakafi.

Maidoki ya bayyana cewar taron wanda Hukumarsa ta shirya na da manufar lalubo hanyoyin taimakawa mabukata. A kan wannan ya bukaci Gwamnatocin Jihohi da su bayar da goyon baya wajen dorewar sha’anin bayar da Zakka a kasar nan.

Taron na kwanaki biyu wanda ke da taken “Hanyoyin Samun Nasara A Sha’anin Bayar da Zakka da Wakafi A Nijeriya” ya samu halartar mahalarta shugabannin Hukumomi da Kwamitocin Zakka da Wakafi daga Jihohin Lagas, Kano, Jigawa, Zamfara, Sakkwato da kuma Gidauniyar Zakka daga Bankin Ja’iz da sauran su.

Bugu da kari duka a ranar ta Litinin, Hukumar Zakka da Wakafi ta rarraba buhu 100 na Alkama ga marasa lafiyar da ke fama da cutar suga ta yadda ko wane marasa lafiya daya ya samu buhu daya da kuma naira dubu 10, 000 domin sayen wake da wasu abubuwan a matsayin gudunmuwar Gwamnatin Sakkwato domin tallafawa sha’anin kiyon lafiya a Jihar.

Maidoki ya kuma bayyana cewar Hukumarsa za ta rarraba naira miliyan biyu a matsayin Zakka ga mutane 50 a fadin Jihar yana mai cewar kowane mutum daya da zai amfana zai samu naira dubu 40, 000 a matsayin jarin karfafa guiwa domin su gudanar da sana’ar da duk suke bukata.

A mabambantan jawabansu, Shugaban Gidauniyar Zakka ta Bankin Ja’iz, Ambasada Adamu Ibrahim da Shugaban Kwamitin Hukumar Zakka na Jihar Jigawa Alhaji Bala Muhammad sun yabawa kokarin Hukumar kan hobbasar kwazon da take yi na taimakawa al’umma.

A wata kuma mai kama da wannan Mai Alfarma Sarkin Musulmi a ranar Talata a Fadarsa ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan kasuwa da su rika bayar da kulawa wajen fitar da Zakka tare da bayar da ita ga wadanda suka cancanta. Sarkin ya bayyana hakan ne a taron da ya jagoranta da ‘yan kasuwar Jihar Sakkwato wanda Hukumar Zakka da Wakafi ta shirya domin wayar da kai da fadakar da ‘yan kasuwa kan wajibci da muhimmancin fitar da hakkin Allah.


Advertisement
Click to comment

labarai