Connect with us

LABARAI

Sabon Albashi Ne Zai Tantance Alawus Din Masu Yi Wa Kasa Hidima –Darakta

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

Babban daraktan hukumar Masu yi wa kasa hidima, Birgediya Janar Sulaiman Kazaure, ya ce, sabon albashin ma’aikatan gwamnati ma fi karanci ne zai tantance karin da za a yi a kan alawus din matasan ma su yi wa kasa hidima.

Babban daraktan ya fadi hakan ne ranar Litinin sa’ilin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan da kammala bukin rantsar da matasan masu yi wa kasa hidima na shekarar 2018, a mazaunin ‘yan yi wa kasa hidiman da ke Kusalla, ta Karamar Hukumar Karayen Jihar Kano.

A cewar shi, “Kokarinmu na ganin an yi wa masu yi wa kasa hidiman kari kan kudaden alawus din su ya haifar da da mai ido. Sakamakon tattaunawar da muka yi ta yi da Ministan Kwadago, Chris Ngige.”

Daraktan ya ce, sam alawus din Naira 18,800 da ake biyan su a yanzun haka, ba zai iya biyan ma su bukatun su ba a lokacin sauke aikin da aka dora ma su na yi wa kasa hidima har na tsawon shekara guda.

“An tabbatar mana da cewa, da zaran an fara amfani da sabon tsarin albashin, za a sake duba alawus din na masu yi wa kasa hidima,” in ji Kazaure.

Daraktan ya bayyana cewa, jimillan masu yi wa kasa hidima dubu 82,000 ne aka aika da su dukkanin sassan kasarnan a wannan shekarar ta 2018, domin a wayar ma su da kai kan aikin, a dukkanin Jihohin kasarnan face wuraren da ke da barazanar tsaro.

A na shi jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bukaci ‘yan yi wa kasa hidiman ne da su guje aikata duk wani abin da zai bata ma su suna da zai iya sabbaba masu takun saka da jami’an su.

Tun da farko da yake maraba da ‘yan yi wa kasa hidiman, daraktan hukumar ta NYSC, ta Jihar ta Kano, Ladan Baba, cewa ya yi jimillan ‘yan yi wa kasa hidima 2,487 ne aka yi wa rajista a mazaunin na su, da suka hada da maza, 1,289 da kuma mata, 1,189.

Mista Baba ya kara da cewa, tun daga lokacin da aka bude matsugunin ‘yan yi wa kasa hidiman makwanni uku da suka shige, ‘yan yi wa kasa hidiman su na ta aiwatar da ayyuka ne daban-daban a matsugunin na su, kuma su na nuna halin kirki.

 


Advertisement
Click to comment

labarai