Connect with us

LABARAI

PDP Ta Soki Yadda Buhari Ya Dora Zargin Kashe-Kashe Ga ’Yan Adawa

Published

on


Daga Muhammad Maitela

Jam’iyyar PDP ta caccaki zargin da fadar shugaban kasa tayi na dora wa bangaren adawa alhakin kashe-kashe da kasar nan ke fuskanta, wanda hakan alama ce karara ta gazawar jam’iyyar APC, mai mulkin gwamnatin tsakiya wajen shawo kan wannan  tabargazar a arewa ta tsakiya, hakan ya tabbatar da rudewar ta da kasa tabuka abin a zo a gani wajen kubutar da halin da kasar nan take ciki.

Bugu da kari kuma, jam’iyyar ta sake jaddada cewa babban abin bakin ne, maimakon ace ta mayar da hankali wajen aiki tukuru dangane da nauyin da ya hau kan ta tare da rungumar kaddarar faduwar da tayi kasa warwas ta nemi agaji, wanda maimakon hakan shugaban kasa Muhammadu Buhari hadi da jami’an sa suka buge da dora zargin wasu dangane da kashe-kashen wadanda ke addabar jama’ar kasar nan kowacce safiyar Allah.

A cikin wani bayani wanda sakataren yada labarai na kasa, a jam’iyyar PDP ya fitar, Kola Olagbondiyan, tare da raba shi ga manema labarai a Abuja, ya ce a cikin yan kwanakin nan shugaban kasa Buhari ya garzaya zuwa wajen Malamin Majami’ar (Archbishop) na cocin Canterbury, Mista Justin Welby, inda ya dora zargi irin na korarren soja ga tsohon shugaban Libiya, marigayi Muammah Gaddafi- bisa wadannan kashe-kashen.

“Shekaru uku da suka gabata, gwamnatin Buhari ta dora zarge-zargen ta ga gwamnatin da ta gabata, da suka kunshi canje-canjen yanayi, rikici a tsakanin manoma da makiyaya, tawayar muhallin noma tare da yawaitar makiyaya da dabbobin su. Yau kuma, an karkatar da lamarin zuwa bangaren adawa tare da dora musu alhakin gazawar da suka yi wajen ceto jama’ar kasa.”

“Wannan babban abin assha ne, wanda maimakon daukar matakan da suka dace wajen tunkarar wannan kalubale wanda yake fuskantar kasa, wanda abin takaici fadar shugaban kasa sai kame-kame da tafiyar hawainiya alhalin kasar mu ta kama hanyar fadawa cikin halin ni’yasu a tarihin kasar mu”.

“Dole ne shugaban kasa tare da ayarin sa a jam’iyyar APC su nada gammon daukar dakon wannan tabargazar kashe-kashen da ta dauki shekaru uku tana daukar rayukan jama’a, a cikin lungu da sakon kasar nan; matsalar da kai tsaye ta fito da rashin kwarewar su ballo-ballo kana da rashin ingantattun tsare-tsaren tafiyar da lamurra tare da babakere da ragontaka wajen tafiyar da mulkin kasa”. Inji shi.

“Wanda zargin baya-bayan nan da ta dora wa yan adawa wata sabuwar makida ce wadda kasasshiyar jam’iyyar APC ta shirya domin ci gaba da karkatar da hankulan yan Nijeriya daga kallon gazawar da ta dabaibaye ta”.

 

“Saboda haka, tabbatacen al’amari ne da zai ci gaba Buhari gindi-a-gindi a matsayin wanda ya kasa wajen cika alkawuran da ya dauka wa yan kasa, sannan da yadda fadar shugaban kasa ke nuna halin ko-in-kula da amfani da rayukan yan kasa a matsayin hanyar siyasa”.

“A matsayin mu na jam’iyya, muna tare da yan Nijeriya, musamman wadanda ake shekar da jinanan su a karkashin gwamnatin APC. Kuma muna yiwa yan Nijeriya marhabin lale, tare da hada hannu wuri guda, domin sake farfado da jam’iyyar PDP wajen yin aiki tukuru da sake dora Nijeriya a sahihiyar alkibla, yanayin da zai samar da sabuwar gwamnati wadda zata iya baiwa jama’a cikakkiyar kulawar da ya kamace su, a wannan babban zabe mai zuwa na 2019”. Ta bakin PDP.


Advertisement
Click to comment

labarai