Connect with us

LABARAI

Kwalejin Shari’a Ta AD Rufa’i Da Ke Misau Ta Fadada Ayyukan Ta Zuwa Karatun Digiri

Published

on


Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Kwalejin Nazarin addinin musulunci da shari’a ta A.D. Rufa’i wato (College of Legal and Islamic Studies) da ke Misau ta samu nasarar fadada ayyukan ta zuwa karatun digiri a karkashin kulawar jami’ar Bayero da ke Kano, don a samu cike gibin karancin guraban karatu da ake fiskanta a jami’oin Nijeriya.

Shugaban Kwalejin Dokta Auwal Ibrahim Amba shi ne ya bayyana haka cikin hirarsa da wakilin mu a ofishin sa da ke Misau inda ya bayyana cewa burin sa da  na sauran malamai da ke kwalejin  shi ne ganin makarantar ta samu ci gaba fiye da yadda ta ke a halin yanzu don haka yake fatar ganin kowane ma’aikaci ya inganta ayyukan sa a wannam makaranta wajen bin doka da yin aiki bisa ka’ida don a samar da karatu mai inganci ga daliban da ke karatu a wannan makaranta. Bayan haka ya bayyana cewa akwai kwasa kwasai da makarantar ke bukatar shigo da su ta hanyar neman hukumomin da suke nazarin yadda ake gudanar da ayyuka a makarantar don amincewa da su a hukumance. Don haka ya ce suna shirye wajen neman amincewar hukumomin da suka dace sun amince da shirin sun a kara yawan kwasa kwasan da suke karantarwa a makarantar don kawo sabbin darussan da ake bukata a wannan makaranta.

Dokta Auwal ya bayyana cewa bunkasa dakunan karatu da tabbatar da kowane ma’aikaci ya rike aikin sa tare da bayar da kulawar musamman wajen samar da kayan aiki da gine gine da ake bukata a wannan makaranta don samun amincewar hukumomin da suka dace don fadada karatun da suke yi a wannan makaranta kamar yadda a halin yanzu aka fara karatun digiri a makarantar.

Dokta Auwal Amba har wa yau ya ba dalibai hakuri game da karin kudin da hukumar makaranta ta yi don a samu ingancin lamurra kuma yin hakan ya taimaka inda makarantar ta samu bunkasa ayyukanta. Ya ce karin da aka yi bai taka kara ya karya ba kuma har yanzu wannan makaranta ke kan gaba wajen biyan kudi mafi karanta cikin manyan makarantun da ake da su a Jihar Bauchi. Ya ce ya kamata daliban su yi la’akari da irin ci gaban da aka samu a makarantar ta hanyar bayar da ilmi kamar yadda kowace makaranta ke bayarwa a Nijeriya.

Don haka ya ce musamman a wannan lokaci da suka fara karatun digiri a wannan makaranta a karkashin jami’ar Bayero da ke Kano akwai babban kalubale da ke gaban makaranta na ganin ta fadada hanyoyin samun kudin shiga don inganta ayyukan ta. Saboda duk takardar digirin da za a yi a makarantar daidai take da wacce aka yi a Kano, kuma ka’idoji da saukin shiga makarantar sun fi sauki da kusanci ga dalibin da ke Jihar Bauchi.  A saboda haka ya yi fatar hukumar TETFUND wato asusun da ke bayar da tallafi kan harkar ilmi a Nijeriya da ya taimaka wajen sa wannan makaranta cikin ayyukan sa don su samu sukunin cin moriyar ayyukan da hukumar ke aiwatarwa na tallafawa manyan makarantu da ke kasar nan saboda yadda kowace makaranta ke karatu take cin wannan moriya haka wannan makaranta ke yi wajen bayar da ilmi. Zaben Kananan Hukumomi Na Nan Daram A Kaduna –Hukumar Zabe

Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

An bayyana cewa zaben Kananan Hukumomi dake tafe a fadin Jihar kaduna, na nan daram babu gudu ba ja da baya, duk da kalubalen da hukumar zaben ke fuskanta na gobarar da ya tashi a ofishin hukumar a makon jiya.  Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Dakta  Saratu Binta Dikko, Shugabar Hukumar Zaben Jihar Kaduna, wanda a turance ake kira da Siecon.

Shugaban hukumar zaben, Saratu Binta Dikko ta bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da aka yi da masu ruwa da tsaki da kuma Shugabanin jam’iyyu, da masu lura da harkar zabe a Jihar Kaduna.

Ta ce Babu maganar dage ranar zaben Kananan Hukumomin da aka sanya zai guda a ranar  12 ga watan Mayu mai zuwa.

Ta kara da bayyana cewa,  “Zamu yi dukkan mai yuwuwa domin tabbatar da adalci, saboda Dimokuradiyya shi ne aiwatar da zabe tare da bayar da sakamakon nasara ga duk wanda ya yi nasara”.

Shugaban hukumar zaben, ta kara da cewa, “duk da mun dan sami ibtala’i na gobarar da ya tashi a wani sashen ofishinmu, amma hakan ba zai hanamu gudanar da zabe kamar yadda muka ayyana a baya ba. Sannan ina kira ga masu cewa wai da wuya mu sami damar gudanar da wannan zabe da ya zo mana a kurarren lokaci, wannan ba gaskiya ba ne, domin babu wani rana daya da muka taba yunkurin daga wannan zabe da muka kudiri aniyar gudanar da shi a ranar 12 ga watan mayu, idan Allah ya kaimu.”

Dangane da maganar da ake yi na cewa ko za’a gudanar da zaben ne da komfuta, kamar yadda hukumar tayi alkawari a can baya. Shugaban hukumar zaben ta bayyana cewa, da wuya zaben ya iya gudana da komfuta kamar yadda aka tsara gudanarwa, saboda a cewarta, rashin amincewar hakan ya biyo bayan kin amincewa da hukumar zaben ta kasa wato INEC, tayi na kin amincewa ayi amfani da mashinan zaben na komfuta, saboda abin da hukumar ta kira, shirye shiryen da take gudanarwa na fuskantar zabukan shekara ta 2019 mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Wadanda suka sami halartar taron sun hada da jami’an tsaro, ‘Yan siyasa, ‘Yan jarida da duk wasu masu jibi da batun zaben,  domin ganin an  tafi tare domin samun  gudanar da zaben Kananan Hukumomi  kamar yadda ya dace.

Duk da wasu da yawa daga cikin mahalarta taron sun nuna gamsuwar su da taron da abin da aka tattauna. Amma a bangare daya kuma, wasu Shugabanin Jam’iyyu sun nuna kin amincewarsu da wannan zabe, kamar yadda Sakataren jam’iyyar APC ya bayyana na cewar, sun rubutawa hukumar zaben takardar korafin cewa, zaben Kananan Hukumomi, yazo dai dai da ranakun gudanar da zabukan Shugabani da Mambobin jam’iyyar APC da za’a gudanar a fadin kasar nan baki daya.


Advertisement
Click to comment

labarai