Connect with us

LABARAI

Kiranye: INEC Ta Kunnowa Dino Melaye Sabuwar Wuta

Published

on


Daga  Sulaiman Bala Idris

Hukumar INEC ta kunnowa Sanata Dino Melaye wata sabuwar wuta, yayin da ta sanya ranar 28 ga watan Afrilun 2018 a matsayin ranar da za ta tantance sa hannun jama’ar da suke da muradin kiranyen sanatan mai wakiltar Kogi ta Yamma.

Sanata Dino Melaye yana Babban Asibitin Kasa dake Abuja, inda yake amsar magani bayan diramar dirowa daga motar ‘yan sanda da ya yi yayin da ake kokarin mayar da shi Jihar Kogi don a gurfanar da shi.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa Babban Kwamishinan INEC na Kasa, Mohammed Haruna ya bayyana batun kiranyen Sanatan a wani taron masu ruwa da tsaki da suka gudanar a garin Lokoja.

Ya bayyana cewa tantancewar kiranye zai kasance ne a runfunan jefa kuri’u 552 a kananan hukumomi bakwai dake karkashin mazabar Kogi ta Yamma.

A ta bakinsa, Mohammed Haruna ya ce, za a fara wannan tantancewa ne daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 2:00 na rana ta hanyar yin amfani da na’urar tantance yatsun wadanda suka sa hannu a takardar neman kiranyen. “Wadanda suka rattaba hannu a korafin kiranyen ne kawai ake sa ran za su je runfunan zabensu don a tantance su.” inji shi


Advertisement
Click to comment

labarai