Connect with us

LABARAI

Kashe-Kashe: Ku Taya Mu Da Addu’a, Koken Osinbajo Ga Shugabannin Coci

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

A ranar Talatan nan ne Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya yi kira ga Shugabannin Coci-Coci na kasarnan da su rungumi hakurin zama da wadanda ba Kiristocin ba, su kuma taya gwamnati addu’an su iya shawo kan barazana da kalubalen da ke fuskantar kasarnan.

Osinbajo, ya yi wannan jawabin ne wajen bikin bude sabuwar shalkwatar Cocin, ‘Deeper Life Bible Church,’ da ke Gbagada, Legas.

“Hakki ne a kan Coci-Coci, su yi wa gwamnati addu’a, da rokon samun agaji ga mahukunta, ba ku yi ta sukan mu ba, a’a, taimaka mana za ku yi da addu’a.

“Wannan wata babban dama ce a gare ni a matsayi na na Kirista. Wannan kafa ce babba na yada sakon Baibul din Yesu Kiristi.”

Osinbajo ya yaba sabon ofishin da aka bude, da kuma yadda aka kawata shi da komai na fasahar zamani, da yadda aka samar da gada da ta hada hanyar, gami da sanya fitullu a kan titunan, wadanda suka dada kawata wajen.

Mataimakin Shugaban kasan, ya yaba wa babban Limamin Cocin, Fasto William Kumuyi, bisa kokarin da yake yi na yada sakon Baibul din Yesu Kiristi.

Ya kuma umurci Coci-Cocin da su tabbatar da akwai kalubale, ya ce, “A yanzun Shedan ya fi kara matsa kaimi, domin karshen duniya ne ke ta kara matsowa.”

A cewar shi, daga cikin tirjiyan da ya kamata Cocinan su yi, shi ne su yi ta gina Cocina, ya ce akwai bukatu masu yawa a kan hakan, wanda Shugaba Buhari ya dora alhakin kula da su a kansa.

“Babban burin Shedan shi ne, ya yi ta haddasa fadace-fadacen Addini a Nijeriya, ta yanda ba wanda zai iya isar da sakon Baibul.

“Jami’an tsaron mu su na bakin iyawan su na kawo karshen wadannan fadace-fadacen. Su na kuma yin duk mai yiwuwa domin ganin an kawo karshen kashe-kashe da sunan fadan makiyaya, Boko Haram, da ma ko fadan mene ne, mu a matsayin mu na Kiristoci bai kamata mu rudu ba.

“An sanya mu ne mu janyo maza da mata zuwa ga samun ceto, hatta su ma su aikata kisan.

“Makiyan mu so suke mu yi ta huduba da a yi kiyayya, amma mu umurnin Ubangiji Yesu Kiristi za mu bi, wanda ya tilasta mana son makiyin mu, mu kuma yi addu’a hatta ga ma su kuntata mana.

“Ba a haifi dan, ko kuma ba za a haifi dan da zai iya hana isar da sakon Baibul din Yesu Kiristi ba,” in ji Osinbajo.

Ya kuma koka kan kashe malaman Addini da kuma jefa Bamabamai a Masallatai da Coci-Coci, ya ce, wannan shi ne makurar ta’addanci.

A cewar shi, ‘Yancin yin Addinin da mutum ya ga dama, ya hada da ‘yancin gina wuraren ibada.

Gwamna Akinwunmi Ambode, na Jihar Legas, ya kwatanta aikin gina Cocin a matsayin wani baban ci gaba, ya kuma yaba ma Cocin kan yadda aka samar da makeken wajen ajiye motoci da gadan da Cocin ya gina wa mutanan Anguwar.

Ambode, wanda Kwamishinan shi na harkokin mata da kawar da talauci, Lola Akande, ta wakilce shi, ya ce, ginin ya dace da yanayin babban birnin.

“Ina kara tabbatar maku da aniyar mu ta samar da daidaito a tsakanin daukacin mazauna Jihar nan.

“Za mu ci gaba da tabbatar da girmama ‘yancin duk mazauna Jihar nan da kuma ba su ‘yancin yin addinin su, mu kuma tabbatar da ba wanda ya ci mutuncin ‘yancin wani.

Babban Limamin Cocin, ‘Redeemed Ebangelical Mission (TREM),’ Bishop Mike Okonkwo, cewa ya yi, wannan hamshakin ginin da aka yi wata karama ce ke kara bayyana, na cewa tabbas Nijeriya za ta sake daukaka.

Okonkwo, ya yi wa kasarnan addu’a na samun nasara bisa dukkanin kalubalen da ke fuskantar ta, yana cewa, face dai taimakon Allah, baccin shi ba abin da wani zai iya yi.

Ya bukaci Kiristoci da su ci gaba da yi wa kasarnan da kuma ‘yan siyasa addu’a, domin samun nasarar fita daga yanayin kuncin da kasar ke ciki.

Tun da farko, a jawabin sa na maraba, Kumuyi, ya ce, an fara aikin ginin Cocin ne a shekarar 2005, sai ya yi wa Allah godiya kan damar da ya ba su na kammala aikin ginin.

“Muna ma Allah godiya, wanda ba kawai ya ba mu damar kammala aiki ne ba, ya ma jagorance mu wajen samun nasarar yin aikin.”

Ya kuma yi addu’an Allah Ya saka wa dukkanin mambobin Cocin na ciki da wajen kasarnan, wadanda da taimakon su ne aka fara aikin har zuwa kammaluwan sa.

Sannan ya yaba wa gwamnatin jihar Legas da mazauna Anguwar ta Gbagada kan irin goyon bayan da suka baiwa aikin, ya ce, Cocin ba za ta manta da hakkin makwabtaka da ya hau kanta tsakanin ta da al’ummar Anguwar ba.

Cocin kuma ta bayyanar da sabon tambarin ta a wajen bukin da manyan mutane da dama suka halarta daga ko’ina.

Manyan malaman Coci maza da mata da suka fito daga nan Nijeriya, Afrika, Kasashen Turai da Amurka ne suka halarci bukin.

Mahalarta taron sun shakata da wake-waken yabo daga kananan yara da samarin Cocin.

Babban ginin Cocin na zamani, yana da girman da zai iya daukan masu ibada 30,000 a lokaci guda, an kuma wadata shi da dukkanin ababen bukata a cikin sa


Advertisement
Click to comment

labarai