Connect with us

LABARAI

EFCC Ta Gufanar Da Sanata Nwaoboshi Gaban Kotu da Zargin Sace Naira Miliyan 805

Published

on


Daga Bello Hamza

Hukumar EFCC ta gurfanar da wani babban jami’in jam’iyyar PDP ta kasa, Sanata Peter Nwaoboshi, a gaban babban kotun tarayya dake Legas ranar Laraba da zargin zamban kudi Naira Milyan 805.

Nwaoboshi, wanda ke wakiltar mazabar Delta ta Arewa a majalisar dattawa ta kasa na fuskantar tuhuma har guda biyu ne wanda suka hada da karkatar da kudade da zamba tare da amfani da wasu kanfanoni masu suna “Golden Touch Construction Project Ltd” da “Suiming Electrical Ltd slammed” wajen aikata wannan danyen aikin,  ya dai musanta dukkan zarge zagen da ake masa nan take.

Bayan daya musanta zargin da ake yi masa ne sai mai gabatar da karar Mista M. S. Abubakar, ya nemi kotu ta aiyana ranar da za a ci gaba da sauraron shari’ar.

Dagan an ne lauyan dake tsaya wa wanda ake zargin Dakta B. J. O. Azinge, ya nemi kotu ta bayar da belin Nwaoboshi ba tare da wani sharadi ba.

Amma nan take lauya mai gabatar da kara ya ki amincewa da bukatar bayar da belin, yana mai cewa, lokaci yin haka bai yi ba saboda jiya jiya aka shigar da karar (ranar 24 ga wata Afrilu).

“A halin da muke ciki masu gabatar da karar ke ci gaba da cika takardun daya kamata na karar da aka kawo”.

Da yake mayar da martini, Azinge, ya ce, an gabatar da bukatar neman belin tun ranar 23 ga watan Afrilu amma suka ki karbar takardar. Ta kara da cewa, ma’aikacin kotun ya yi kokarin mika musu takardar a ofishinsu amma suka ki karba.

Daga nan sai ta ce, “Ba zai yiwu a bata wa kotu lokaci ba, an dade da gabatar da tuhumar, kotu zata iya bayar da belin sannan a ci gaba da jiran masu gabatyar da karar har sai sun gama shiryatakardunsu”

Da yake mayar da martini, mai gabatar da kara, ya yi korafin cewa, shi bai san hukumar EFCC ta ki karbar takardar sanarwar da aka aika mata ba.

Ya kara bayyana cewa, kamar yadda tuhumar ya nuna ya kamata ne a gabatar da takardar ne a garin Abuja ba wai a ofishin hukumar na Legas ba.

Ya ci gaba da cewa, koda an gabatar da takardar yadda ya kamata, lokacin sauraran maganar belin bai yi ba saboda doka ta bayar da wa’adin kwanaki biyu ne kafin a fara sauraron maganar belin.

Daga nan kuma ya ce, masu gabatar da kara basu gama cikakken shirin ci gaba da shari’ar ba, amma kotu tana iya dakatar da karar in har wadanda ake kara ya bukaci haka.

Rohotanni ya nuna cewar, nan take alkalin kotun mai shari’a Mohammed Idris ya dakatar da sauraron karar zuwa karfe 11.00 na safe domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Takardar karar da hukumar EFCC ta mika wa kotu mai namba FHC/L/117C/2018, ya nuna cewa, wanda ake zargin ya aikata wannan laifin ne tsakanin watan Mayu da Yuni na shekarar 2014 a Legas.

Bayanai sun nuna cewar, Nwaoboshi, ya sayi wani katafaren gida da ake kira Guinea House a Appa Legas a kan kudi Naira Miliyan 805 duk daya sane da cewar Naira Miliyan 322 daga cikin kudaden an same sune bata hanyar day a dace ba. An yi amfani da kanfanin  Suiming Electrical Ltd. Wajen aika wad a kudaden a ranar 14 ga watan Mayu 2014, abin dake nuna cewar kanfanin Suiming Electrical da Nwaoboshi da kuma kanfanin Golden Touch suka hada hannu wajen aikata wannan laifin, hakan kuma ya saba wa sashi na

15(2) dana (d) 15 dana (3) da kuma na 18 (a) na dokan cin hanci da rashawa na “Money Laundering (Prohibition) Act 201”.


Advertisement
Click to comment

labarai