Connect with us

LABARAI

2019: Gwamnonin APC Sun Amince Da Takarar Buhari

Published

on


Daga Bello Hamza

Dukkan gwamnoni 24 da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC sun nuna amincewar su a kan aniyar takaran kujerar shugabancin kasar nan da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a zabe shugaban kasa na shekara 2019 dake tafe.

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ne ya bayyana wa manema labarai bayan taron sirrin da suka yi da shugaban kasan a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Talata.

A taron shugabannin jam’iyyar ne da aka yi kwanakin baya, shugaban kasa ya baiyana aniyarsa na sake neman takarar kujerar shugaban kasa a karo na biyu a zabe mai zuwa na shekara 2019.

Mista Okorocha, ya sanar da Manama labaran cewa, sun sanar da shugaban kasar aniyarsu na mara masa baya a aniyarsa na sake neman takarar kujerar shugabancin kasar nan a taron da suka yi a fadar shugaban kasan.

“Mun zo uyi masa brka da dawo wa daga tafiyar day a yi da kuma jinjina masa a kan karfin haklin da yai na bayyana aniyarsa na sake neman takarar kujerar shugabancin kasar nan, abin da kuma mu gwamnoni 24 na jam’iyyar APC ke goyon bayansa a kan wanna  hankoron”.

“Mun kuma zo ne domin karfafa shi a kan ya ci gaba aiyukan san a alhairi da kokarin da yake yin a ceto Nijeriya daga halin da take ciki” inji shi.

Ya kara da bayyana cewa, taron ya kuma tatauna shirin da ake yi na babban taron jam’iyyar na kasa da ake yi da kuma zabukkan shugananin jam’iyyar da ake shirin yi a dukkan matakai, da kuma fatan a gudanar dasu ba tare da wani matsala ba.

Ya ce, shugaban kasan da gwamnonin sun yanke shawarar hada hannun domin fito da tsayayyen shugaban jam’iyyar da zai iya samar da nasara a zabukkan dake tafe.

Daga nan ya kuma ce, “Mun amince da ba za mu yarda batubn ‘yan takara masu yawa su bata mana jam’iyya ba”

Gwamnan, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ya karyata maganan da ake yin a cewa, an shirya taro ne domin aiyana goyon baya ga tsohon gwamnan jihar Edo a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa a babban taron jam’iyyar da za a gudanar nan gaba.

Ya kara da cewa, nan gaba kadan kungiyar gwamnonin zasu bayyanan matsayinsu a kan batun shugabancin jam’iyyar, zasu kuma sanar da jama’a a lokacin day a dace.

Sakataren gwamnatin tarayya, wanda yana cikin malarta taron ya ce, sabbin shugabanin jam’iyyar APC na makin kananan hukumomi da jihohi  har zuwa matakin tarayya da za a zaba a kwananna, za a fito dasu ne ta hanyar yarjejeniya ba tare da anyi zabe ba.

Wadanda suka halarci taron  sun hada da mataimaki shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da kuma shugaban ma’aikatan ofishin shugaban kasa  Abba Kyari.

Gwamnonin jam’iyyar APC da suka halarci taron sun hada da Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da Yahaya Bello na jihar Kogi da Simon Lalung na jihar Filatoda  Jubrila Bindow na jihar Adamawa da Abdulaziz Yari na jihar Zamfara.

Sauran sun hada da Rochas Okorocha na jihar Imo da Abdulahi Ganduje na jihar Kano da Kashim Shettima na jihar Borno da kuma Abubakar Sani Bello na jihar Niger da Tanko Almakura na jihar Nassarawa da Abiola Ajimobi na jihar Oyo da Ibikunle Amosun na jihar Ogun da Godwin Obaseki na jihar Edo da kuma Abubakar Badaru na jihar Jigawa.


Advertisement
Click to comment

labarai