Connect with us

LABARAI

Za A Yi Zaben Kasuwar Galadima Cikin Mutunta Juna –Alhaji Mustapha

Published

on


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Daya daga cikin masu neman takarar shugaban kungiyoyin yan kasuwar Galadima Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya bayyana cewa babbar manufarsa na takarar shi ne tabbatar da hadin-kai dan kawo cigaban bunkasar harkokin kasuwancin dukkanin bangarorin ‘yan kasuwar da hakan zai taimaka wajen cigaba da bunkasa kasuwancinsu da tattalin arzikin jahar Kano.

Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman wanda ya ce ya shiga takara ne a sakamakon amsa kiran da ‘yan kasuwar suka yi masa na cewa lallai ya fito neman takarar shugabancin kungiyoyin yan kasuwar ta Galadima.

Ya yi nuni da cewa dukkan burinsu a matsayinsu na yan kasuwa da suke takarar bai wuce na kawo cigaba a kasuwar ba, don haka kowa ka gani ya fito takara yanada tasa irin gudummuwa da yake gani zai bayar ne don ci gaban kasuwarsu ta Galadima.

Alhaji Mustapha ya ce don haka nema da ‘yan kasuwar suka matsa ya fito ya amsa musu ganin cewa sun jin yanada irin tasa gudummuwa dazai iya bayarwa ga cigaban kasuwancinsu idan ya zama shugabanta.

Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya ce shi dama yana bada gudummuwa don ci gaban kasuwar a fannoni da dama hatta sabuwar kofar Galadima da aka gina shiya jagoranci a gina shi.

Bayan nan akwai aikin sanya fitilu da ya nemo daga Gwamnatin jahar Kano da za a yi a cikin kasuwar karkashin ma’aikatar kasuwanci jahar Kano nan bada jimawa ba za a soma aikin.

Akan harkar kulada tsaron kasuwar kuwa ya ce su a banfarensu na yan’masu saida manja a kasuwar su suke cika kudinda ake biyan masu kulada tsaron kasuwar idan an tattara a wajen kungiyoyi bai cika ba a biya masu gadi.

Alhaji Mustapha Shu’aibu Sulaiman ya ce ko a kokarin rage cunkosa a titin Galadalima inda kasuwar tasu take yana fitowa ne ya tsaya dan tabbatar da ba’a sami cunkuso ba, sannan kuma duk wani korafi na yan kasuwar ko wata matsala data taso ya kan yi iya kokrinsa dan ganina an sami maslaha a tsakani.

Alhaji Mustapha ya yi kira ga yan kasuwar akan su sani duk wanda ke cikin wannan takara da suke ya shigane saboda kishin yanda zai taimakawa cigaban kasuwancinsu, ba abu ne na a yi rai ko kar a yi rai ba, duk wanda Allah ya baiwa ya kamata a hadu a bashi cikakkiyar hadin-kai da goyon baya dan cimma nasara a kasuwar.

Mustapha ya yi kira ga yan kasuwar Galadima akan su yi zabe cikin girmama juna da mutuntawa ba tare da wata matsala ba, don dukkan yan kasuwar dama suna zaman tare da girmama juna a harkokinsu na kasuwanci.


Advertisement
Click to comment

labarai