Connect with us

LABARAI

Tinubu Ya Taya Oyegun Murnar Nadin Yan Kwamitin Shirya Taron Jamiyyar APC

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

 Jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu ya taya jam’iyyar murna a bisa kafa Kwamitin da zai shirya babban taron jam’iyyar da zabukan da za a gudanar a sassan kasar nan.

Ya yi wannan sanarwar ne ta bakin jami’in watsa labaransa ranar Litinin, Mista Tinubu ya ce, wanna shirin da jam’iyyar APC ke yi duk da matsalolin da take fuskanta wani alamine na yunkurin tabbatar da mulkin dimokradiyya.

“Ina taya shugaban jam’iyyar mu tare mambobin Kwamitin zartarwa da kuma yan kwamitin shirya babban taron da aka rantsar a bisa wannan nasara da aka samu,” Inji Tinubu.

“Shugaban kwamitin kuma gwamnan Jihar Jigawa Abubakar Badaru, mutum ne tsayayye mai mutunci da zai iya gudanar da wannan aiki da aka dora masa.

“Tare da hadin kan sauran mambobin kwamitin ina da tabbacin za a gudanar da tatukan jam’iyyar muya dukkan matakai cikin nasara ba tare da wani matsala ba” inji shi.

Shugaban jam’iyyar APC Mista John Odigie-Oyegun, ya kaddamar da kwamitin mutum  68 domin shirya babban taron jam’iyyar ta kasa wanda za a gudanar ranar 14 ga watan Mayu.

A taron kaddamar da yan kwamitin da aka yi a Abuja,  Mista Odigie-Oyegun ya bukaci Kwamitin ta tabbatar da duk wani dan jamiyya ya samu daman yin takara kujerar da yake so in har yana bukata.

“A yau Ina mika maku ragamar tafiyar da komai, a karshe babban taron kuma ina fatan za a samu dunkulalliyar Jamiyya karkashin duk wanda Allah Ya bai wa jagorancin jam’iyyar” inji Mista Odigie-Oyegun.


Advertisement
Click to comment

labarai