Connect with us

LABARAI

Sama Da Asibitoci 700 Suka Amfana Da Garabasar Maganunuwa A Jihar Kano – Getso

Published

on


Daga Abdullahi Sheka Kano

Asibitoci 700 daga cikin cibiyoyin lura da lafiya 1,000 a Jihar Kano suka amfana da shirin samar da maganunuwa masu rangwame, Jawabin haka ya fito daga bakin Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso lokacin da yake karbar bakuncin tawagar jami’an lafiya daga Jihar Zamfara karkashin Jagorancin Kwamishinan Lafiya na Jihar ta Zamfara Alhaji Lawal M.  Liman a ofishinsa. Shirin na  DRF  wani shiri ne da aka kirkira a shekarar 2007 wanda ya hada da samar da maganunuwa  daga ma’aikatar lafiya zuwa asibitocin Jiha domin marasa lafiya su saya a farashi mai sauki domin tabbatar da ingantacciyar lafiya.

Kamar yadda kakakin hukumar lafiyar na Jihar Kano Sama’ila Garba Gwammaja  ya bayyanawa manema labarai cewa, Kwamishinan ma’aikatar Lafiya na Jihar Kano ya bayyanawa tawagar da ta ziyarce shi daga Jihar Zamfara yadda Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ke gudanar da wannan shiri duk da yawan al’ummar Jihar Kano. Yace hukumar Lafiya a Jihar Kano na bada kulawa ta musamman yadda tsarin ke samun nasara yadda ya kamata.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya nuna farin cikinsa bisa wannan ziyara, sannan kuma ya tabbatarwa da tawagar data ziyarce shi daga Zamfara, ya kuma jadadda a niyarsa ta bayar da dukkan bayanan da suke bukata wadda zasu taimaka masu domin farfado da nasu tsarin lafiyar a Jihar Zamfara.

Da yake gabatar da na sa jawabinsa Kwamishinan Lafiya na Jihar Zamfara  ya bayyana cewa sun zo Jihar Ksno ne domin tattauna hanyoyin da Jihar Kano tabi wajen inganta harkar lafiya, saboda haka sai ya jijinawa Gwamantin Kano bisa tagomashin da harkar Lafiya ya samu kamar yadda Jihar Kano ta zama a bar koyi a tsaknin sauran Jihohin Kasar nan.

An Yi Taron Addu’ar Dakarun Yakin Neman Zaben Takai Da Suka Kwanta Dama A Kano

Daga Mustapha Ibrahim Kano

A wannan lokaci ne saktarori da jami’an yakin neman zaban Malam Sagir Takai  wanda yayi Takarar neman zama Gwamnan Jahar Kano a 2011 da 2015 a Jam’iyyar ANPP da PDP sukayi taron yiwa masoya da jami’an yakin neman zaban Malam Sagir Takai wadanda suka kwanta dama Addu’ar neman Rahama da kuma Allah ya gafarta musu zunuban su da sukayi a lokacin Rayuwar su.

Taron wanda akayi shi karkashin shugabancin Yunusa Yusha’u Albasu ya sami halartar daukacin saktarori da Jami’an tsare tsaren yakin neman zaban Takai a wannan lokaci da kuma tsofin shugaban kananan Hukumomi na Jam’iyyar ANPP na kananan Hukumomi 44 na Kano musamman wanda suke tare da Takai a Jam’yyar su ta PDP a Kano.

Shima tsohon shugaban karamar Hukumar madobi Honorabul Ibrahim Mu’azu Madobi ya bayyana cewa ba shakka wannan taro ya dace da a shirya shi a wannan lokaci kuma hakan na nuna cewa Jam’iyyar su ta PDP na samun cigaba sosai kamar yadda ya kamata a matakin Kano da Kasa baki daya.

Haka kuma ya bayyana cewa alkawarin da Jam’iyyar APC ta yiwa mutanan Najerya to har yanzu bata cika shi ba idan akayi la’akari da abubuwan da suke faruwa a kasa musamman kamar Biniwai, Zamfara, Kaduna, Katsina, Kogi, Barno, Adamawa da dai sauran Jahohi da ake jin labara mara dadi na kashe kashe da kuma satar mutane dan haka akwai bukatar Jam’iyyar APC ta cika alkawarin da ta yiwa al’ummar Najeriya ta hanyar bunkasa Tattalin Arziki da kuma adalci na tohumar wanda ake zargi a kowacce Jam’yya ne ba a rika kama Yan PDP ba ana barin Yan APC ba


Advertisement
Click to comment

labarai