Connect with us

LABARAI

Nijeriya Ta Nuna Fusatar Ta Kan Kashe Wani Dan Nijeriya A Afrika Ta Kudu

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

Ofishin jakadancin Nijeriya a kasar Afrika ta kudu, ya ce, ya rubuta takardar koke ga hukumomin kasar kan kisan da aka yi wa wasu ‘yan Nijeriya kwanan nan a can.

Wasu fusatattun ‘yan kasar ta Afrika ta kudu, sun kona wani dan Nijeriya mai suna, Clement Nwaogu, a garin Rustenburg, da ke arewa maso yammacin yankin Afrika ta kudun a ranar Lahadi. Kisan na shi ya biyo bayan kisan da aka yi wa wani dan Nijeriyan ne mai suna, ThankGod Okoro, 30, dan asalin Jihar Enugu, kwanaki 10 da suka shude.

Wannan kisan na baya-bayan nan ya janyo fusatan sauran al’ummar Nijeriyan da ke zama a Afrika ta kudun, wanda ta kai su ga yin jerin gwano zuwa Ofishin ‘yan sandan garin domin jin bahasi.

Ofishin jakadanci ya ce, ya tura jami’an sa can domin su kwantarwa da al’umman Nijeriyan hankali.

“Jakadan mu yana lura da komai. Ya yi magana da ‘yan Nijeriyan ya kuma aika da jami’an sa don su kwantar ma su da hankali,” in ji Mista Godwin Adama, na ofishin jakadancin.

“A gobe da safe ne za mu tattauna da shi kan lamarin. Ya ma rubuta wa gwamnatin kasar wasika kan batun, muna sauraron amsar su ne, domin mu san mataki na gaba,” In ji shi.

Ya ce, kuskuren da suka yi shi ne, na zaton cewa yana fataucin muggan kwayoyi ne, amma ba su san shi Clement Nwaogu, cikakken dan kasuwa ne ba.

Jami’in ofishin jakadancin ya yi nu ni da cewa, har yanzun ana tsare da ‘yan Nijeriya 13 bisa zanga-zangar da su ka yi ta nuna rashin amincewar su da hare-haren da ake kaiwa ‘yan Nijeriya.

Ya ce, garin na Rustenburg, da kisan na baya-bayan nan ya faru, suna da muguwar kiyayya da ‘yan Nijeriya, hatta jami’an ofishin mu da Lauyoyi sai an hada su da rakiyar ‘Yan sandan mu in za su je shari’ar su.

Babbar mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin kasashen waje, Uwargida Abike Dabiri-Erewa, ta bukaci da a sake duba matsayin kasashen biyu.

A bara ne dai kasashen biyu suka sanya tsarin lura da kiyaye ‘yan Nijeriyan daga hare-haren ba gaira-ba-sabar.

Ta kuma kirayi gwamnatin ta Afrika ta kudu da ta nemo hanyar kawo karshen kashe-kashen na ‘yan Nijeriya a kasar na ta.

Ta kuma bukaci daukacin ‘yan Nijeriya da ke da zama a wajen kasarnan da su zama ma su bin doka da oda gami da kiyaye aikata laifuka a duk inda suke domin su kaucewa kowane irin hari ko kisa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai