Connect with us

LABARAI

Nijeriya Ce Babban Birnin Talauci Ta Duniya –Farfesa Moghalu

Published

on


Dan takarar Shugaban Kasar Nijeriya, Farfesa Kingsley Moghalu ya bayyana cewa, Nijeriya ce Babban Birnin Talauci ta duniya.

Farfesa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin ta ‘ChannelsTb’ a shirinsu mai taken ‘Sunday Politics’ na ranar lahadin da ta gabata.

Mai gabatar da shirin, Seun Okin ya tambayi Farfesan dangane da abin da yake nufi da ya ambaci Nijeriya da ‘Babban Birnin Talauci Ta Duniya’.

Farfesan ya bayyana cewa; “Yan Nijeriya sun jima cikin kangi daga hannun ‘yan siyasar da suka mayar da abin nasu tamkar wani gado. Wadanda su burinsu kawai shi ne su biya bukatun kashin kansu. Don haka idan ka hada gabadaya wadannan halayya wuri guda, babu abin da za su haifar sai talauci. Wannan shi ne dalilin da ya sa a yau, Nijeriya ce babbar birnin talauci ta duniya. Nijeriya ce ke da mafi yawan adadin mutanen da ke fama da kangin talauci a duniya a yanzun.

Mun jima da shan gaban Kasar Indiya a yawan talakawa. Duk da fa cewa, Indiya ta ninka Nijeriya sau shida a yawan mutane. Amma duk da haka mun fi su yawan talakawa.

“Wannan shi ne abin da ya sa na yi imani da cewa, ana bukatar wani irin gagarumin sauyi a yanayin gudanarwar Nijeriya. Muna bukatar sauya akalar tafiyar kasar daga kangin talauci zuwa wadata. Muna bukatar a tseratar da Nijeriya daga rarrabuwar da ‘yan kasa ke fama da ita zuwa hadin kai da zaman lafiya.” Inji shi

Yayin da aka tambayi Farfesan ta yadda zai iya saita lamarin Nijeriya matukar ya samu nasarar amsar mulkin kasar a shekarar 2019. Farfesan Ya bayyana cewa, ya kwashe tsawon shekarunsa ne a matsayin jami’in Majalisar Dinkin Duniya wanda ke aikin farfado da kasashen da suke fuskantar matsaloli daban-daban.

Ya ce; “Kamar a yanzu, Nijeriya kasa ce ta ke fuskantar matsaloli wacce ke bukatar a farfado da ita. Ni babban burina shi ne bunkasa Nijeriya, a gina ta, a kuma ceto ta daga barazanar da take fuskanta.

“Zan yi kokarin nunawa ‘yan Nijeriya irin kasar da ake bukata. Idan muka samu damar mulkar kasar nan, za mu tabbatar da mun wadatar da ayyukan yi, bunkasa kiwon lafiya, samar da wadatattun hanyoyi, da sauransu. Wannan shi ne abin da za mu kawowa Nijeriya.” Inji shi.

Daga karshe, Farfesa Moghalu ya bayyana cewa, a wata mai kamawa ne zai ayyana jam’iyyar da zai tsaya takara a cikinta.


Advertisement
Click to comment

labarai