Connect with us

LABARAI

Muna Rokon Buhari Ya Turo Jami’an Tsaro Na Gaggawa Nasarawa – Maku

Published

on


Daga Daga Zubairu T M.Lawal Lafia

 

Tsohon Ministan yada labarai a zamanin Gwamnatin Jonathan kuma Dan Takarar Gwamnan Jihar Nasarawa karkashin Jam’iyyar APGA Hon. Labaran Maku ya yi roko ga gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammad Buhari da a taimaka a kawo Jami’an tsaron sojoji domin kare Jihar Nasarawa daga bala’in da take fuskanta na zubar da jini.

Labaran Maku ya ce; al’umman yankin Nasarawa ta kudu dake karkashin Kananan hukumomi guda biyar Lafia, Doma, Awe, Obi, Keana mazauna wadanan yankuna na cikin hadari.

Ya ce; “A kowacce rana ana zubar da jinanen mutanen da ba su ji ba basu gani ba. Yanzu haka kauyuka ba su shiguwa ta dadi musamman kauyukan yankin Obi da Keana da Doma an tarwatsa mazauna gurin an kashe na kashewa an barnata dukiyoyi.”

Labaran Maku ya kara da cewa; batun maganar gona a bana Allah kadai ya san yadda lamarin zai kasance saboda manoma dake kauyuka ana karkashe su ana lalata gonakinsu ana kona gidajensu.

Ya kara da cewa, yanzu ‘yan kabilar TB rayuwarsu tana cikin barazana saboda ana kashe su ana kashe mata ana kashe maza da yara Kanana. Amma babu wani matakin a zo a gani wanda Gwamnatin Jihar Nasarawa ta dauka domin kare rayukan wadannan mutanen.

Labaran Maku ya ce; a shekarar 2001 an taba samun makamancin irin wannan rikicin a Jihar Nasarawa lokacin yana Kwamishinan yada Labarai na jihar .an dauki tsawan watanni an wannan rikicin hartakaiga an kashe Sarkin Azara lokacin Gwamna Abdullahi Adamu ya nada kwamitin yadda za a samar da karshen wannan rikicin ina cikin wannan Kwamitin Sarkin Lafiya da Sarkin TOR TB da mukaddashin Gwamna munyi aiki birni da kauye munzaga kauyuka muna zantawa da jama’a. Haka muka yi ta jin ra’ayin jama’a har muka samo bakin zaren aka magance matsalar wannan rikicin.

Maku ya ce; “Me ya sa tun daga wannan lokacin ba akara samun wani rikici a Nasarawa ba har Abdullahi Adamu ya kammala Gwamna shekara takwas Ali Akwe Doma ya hau shekara hudu ba ayi wani rikiciba sai daga 2012 aka fara rikici a wannan jihar  tsawan shekara goma jihar tana zaune Lafiya amma zuwan wannan Gwamnan tun daga 2012 ake zubar da jini  har yanzu jihar Nasarawa ta kasa zaman Lafiya.

“Yanzu irin kisan gillara da ake yi a Nasarawa abin babu kyaugani ana kashe mutane. ‘Yan kabilar TB suna da hakki  kan Gwamnati ta kare Lafiya su tunda suma mazauna jihar ne. Labaran Maku ya ce yanzu Jihar Nasarawa na cikin barazanar fadawa mawuyacin hali al’umman jihar suna cikin rudani kullum sai kaji an kashe mutum  70 ko 30 aikin kenan.

Ya kamata Buhari ya turo Jami’an tsaro a Nasarawa idan yanason jama’a su rayu. Kuma Jami’an tsaro su kasancene a kauyuka guraren da ake rikicin saboda yin hakan zai sanya jama’a su koma garuruwansu su zauna cikin Aminci da nutsuwa su yi noma.” inji shi

Da yake magana dangane da jifan da yan gudun hijira suka yi wa Gwamna Al-makura ranar Talata da tagabata a garin Agwatashi dake Karamar hukumar Obi. Maku ya ce; “ai wannan abin da aka yi bashi da halaka da yan siyasa babu dan siyasan da zai sanya aje a jefi Gwamna saboda wannan san ba gaskiya bane.

Amma abin la’akari anan shine mutanen dake sansanin yan gudun hijirar nan an korosune daga gidajensu akwai wadanda aka kashe mazajensu, akwai wadanda aka kashe matayansu da ya’yansu. Akwai wadanda aka kashe yan uwansu kuma an kona garuruwansu sun sha da kyar suka zo nan. Gwamnati bata iya tura Jami’an tsaro sun kare su daga kisa ba.

“Sai gashi Gwamna shi kadai da tarin Jami’an tsaro suna iyamasa rakiya ai dole ran mutanen nan ya baci. suka jefi Gwamna saboda idan da irin wannan Jami’an tsaron da suka yi wa Gwamna rakiya me ya sa ba za a tura su su kare rayukan jama’a ba.

“Wannan ma kadai zai iya tunzura mutane su jefi Gwamna. Ai ko ma’aikatan Gwamnati idan suna yajin aiki suna zanga-zanga idan sun ga kayan Gwamnati suna lalatawa ne saboda bacin rai.” inji shi

Labaran Maku ya shawarci Gwamna Al-makura ya yi kokari ya san hanyar da zai samar da zaman Lafiya a jiahr Nasarawa kafin zaben 2019. Ya ce, ya kamata Gwamna Al-makura ya dauko aikin gwamnatin da ta gabata a 2001 ya duba aikinta na zaman Lafiya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai