Connect with us

LABARAI

Kasar Switzerland Ta Dawo Da Dala Miliyan 322.5 Na Kudaden Da Abacha Ya Sata – Jakada

Published

on


Daga Bello Hamza

Kasar Switzerland ta bayyana cewar, ta mayar da dukkan kudaden da tsohon shugaban kasa marigayyi Janar Sani Abacha ya boye a kasar har da karin ruwan Dala Miliyan 1.5.

Ambasada Pio Wennubst, mataimakin darakta kuma shugaban Global Cooperation Department da Swiss Agency for Debelopment and Cooperation, ne ya bayyana wa wakilinmu wannan batun a garin New York ta kasar Amurka.

Wennubst ya ce, kasar  Switzerland ta dawo da kusan Dala Miliyan 322.5 (Naira Biliyan 116.11) ga gwamnatin tarayya. Ya kara da cewa, asalin kudaden da Abacha ya boye a kasar sun kai Dala Miliyan 321.

Tuni gwamnatin tarayya ta sanar da karban Dala Miliyan 322.51 daga hannun gwamnatin kasar  Swiss daga cikin kudaden da aka kwato wanda marigayyi tsohon shugaba kasa Sami Abacha ya sata.

Ministan kudi Misis Kemi Adeosun, ce ta tabbatar da karban kudaden daga kasar Switzerland ta hannun jami’in watsa labaran ta, Mista Oluyinka Akintunde.

Akintunde ya ce, “Mun sanar da cewar, mun karbi Dala 322,515,931.83 (N116,105,735,458.80) in da muka zuba a asusu na musamman a babban Bankin Nijeriya  (CBN) a ranar 18 ga watan Disamba 2017 daga gwamnatin Swiss”.

Da yake tabbatar da wannan, Wennubst ya ce, “Mun dawo da Dala Miliyan 321 har da kudin ruwa na Dala Milyan 1.5 na  ajiyar kudaden.

“Mun dawo da dukkan kudaden kusan Dala Miliyan 322.5 tare da ruwan da kudin suka kawo a lokacin da aka kullesu’’.

Jakadan na kasar Swiss, ya kuma kara da cewa, an mayar wa da gwamnatin Nijeriya kudaden ne ba tare da wani sharadi ba.

“Babu maganar wani sharadi amma a kwai wani shiri na tallafawa jama’a da gwamnatin tarayya dana Bankin Duniya suka fito da shi da zai yi amfani kwarai da gaske.

“Bayan tattaunawar da muka yi sharadin da sashin sharia suka aiyyana shi ne bukatar Bankin Duniya ya zama mai lura da yadda aka dawo da dukiyar, abin da muke aiki a kai kenan’’.

Ya ce, wadannan kudaden na cikin gudummawar gwamnatin tarayya a kan samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasa a shirin da aka sa wa suna “plus concessional loans from the Bank”.

Idan za a iya tunawa kotun kasar Swiss ce ta karbe kudaden da Marigayi Janar Sani Abacha ya Sata bayan takaddamar shari’a da aka yi da dansa Abba Abacha  a shekarar 2014.

Tun asali an boye kudaden ne a Ludembourg, suna cikin yan kalilan din biliyoyin dalolin da ake zargin Abacha ya Sata a lokacin da yake mulki tsakanin shekarar 1993 zuwa 1998.

Haka nan kuma, gwamnatin kasar Birtaniya ta sha alwashin dawo wa Nijeriya da dukkan kudade da kaddarorin da aka sata a ka kuma shigar dasu kasar ta barauniyar hanya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai