Connect with us

LABARAI

An Rantsar Da Shugaban Sabuwar Kungiyar NKKDD A Kano

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

An rantsar da Alhaji Haruna Abdullahi a matsayin zababban sabon shugaban kungiyar masu sayar da Nama, Kaji, Kayan Miya, Abinci, Dankali da Doya ta Post Office Traders Debelopment Association da masu taimaka masa su shida shugaban wanda aka rantsar tare da masu taimaka masa yayi alkawarin kawo sauye sauye da kuma cigaban wannan kungiya cikin gaggawa bisa yardar mai duka da kuma taimako da hadin kan sauran shugabannin kungiyoyin da aka zaba wanda zasu ja ragamar wannan sabuwar kungiya ta wadan nan Yan kasuwa da suke Titin Post Office da ke Kano.

Su dai shugabannin wannan kungiya da aka zaba sune Malam Mustapha Falalu, Alhaji a matsayin mataimakin shugaba, Malam Jinjiri Ado sakatare Malam Muahammad Nura Jami’in hulda da jama’a na kungiyar (P.R.O) Alhaji Hassan Shehu mai binciken kudi na kungiyar NKKDD Malam Abdulhamidu Idris a  matsayin ma’ajin kudi wadan nan sune shugabanni da aka zaba kuma a ka rantsar da su a Babban Filin da ke kusa da wannan kasuwa da ke Kano.

Tun farko a jawabinsa Alhaji Haruna Abdullahi yayi alwashin yin aiki ta hanyar kwatanta gaskiya da adalci ba tare da san zuciya ba in da yayi alkawarin yin aiki hannu da hannu da shugabannin kungiyar da aka zaba kuma aka rantsar a yau inda kuma ya yabawa duk kannin Hukumomi da suka taka rawa wajan tabbatar da yin wannan zabe lami lafiya inda kuma ya jaddada mahimmancin kungiya a irin wannan lokaci da mahimmancin da iyayen kungiyar ke dashi a Rayuwar Al’umma kamar irin su Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da mai Martaba Malam Muhammadu Sunusi II inda yayi fatan alkairi ga sauran iyayen kungiyar na kusa da nesa domin irin rawar da suka taka na komai ya tafi lafiya.

Shi kuwa jagoran Rantsuwar da shugabannin wannan kungiyar nasiha yayiwa shugabanni da mabiyan su akan sanya tsoran Allah da yin gaskiya komai dacin ta taron rantsuwar dai ya samu halartar mahimman mutane da gabatar da jawaban su daban daban ciki kuwa harda kallabi tsakanin Rauwuna Hajiya Mai Fura ta Kasuwar Post Office Kano.

 


Advertisement
Click to comment

labarai