Connect with us

WASANNI

Yanzu Babu Wata Matsala Tsakanina Da Mourinho, Inji Conte

Published

on


Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Antonio Conte, dan kasar Italiya ya bayyana cewa kawo yanzu babu wata rigima ko rashin jituwa tsakaninsa da mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho.

Conte ya bayyana hakane a wata hira da manema labarai bayan kungiyarsa ta lallasa Southampton daci 2-0 a wasan kusa dana karshe na cin kofin kalubale na FA na kasar ingila wanda hakan yake nufin kungiyoyin Chelsea da Manchester United zasu hadu a wasan karshe a wata mai kamawa.

Yaci gaba da cewa tsakaninsa da Mourinho yanzu babu komai saboda kowa yanason kungiyarsa ta lashe kofi ne kuma kowanne yanason ace kungiyarsa ce babba a kasar ingila saboda haka kowa yan akare kungiyar da yakewa aiki ne.

Ya kara da cewa yana girmama Mourinho sosai saboda mai koyarwa ne wanda yasan abinda yakeyi kuma yana girmama kungiyar Manchester United saboda irin tarihin da take dashi a duniya kamar yadda yasan Mourinho yana girmama kungiyarsa.

A karshe yace yana fatan doke Manchester United domin lashe gasar ta FA domin bayason kammala kakar wasan wannan shekarar batare da wata gasa ba.

A ranar 19 ga watan Mayu mai zuwa ne dai kungiyoyin zasu hadu a filin wasa na Wembley domin buga wasan na karshe.

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai