Connect with us

LABARAI

Yanayin Yadda Wata Makarantar Sakandare Take Cikin A Kebbi

Published

on


Jama’a dai nata ci gaba da tofa albarkacin bakunansu kan yanyin yadda wasu makarantun sakandare suke cikin a jihar Kebbi, musamman makarantar sakandare da ke barikin soja malakar gwamnatin jihar ta Kebbi.

Duk da cewa gwamnatotin arewacin kasar nan na nuna cewa suna kula da kuma ba ilimi muhimmanci a yankunansu har a kasafin kudi tun daga shekarar ta 2015 har zuwa shekara ta 2018, za ka ga cewa ilimi ne ke kwashe kaso mafi yawa. Ko a kasafin kudi na shekara ta 2018 a jihar ta Kebbi ilimi ne ya lashe kaso mafi tsaka daga cikin kasafin na bana, amma duba da irin kasafin kudin da ilimi ke lashe wa amma har yanzu babu dankunan karatu masu inganci a wasu jahohin arewacin kasar nan.

Wasu masana harakar ilimi a jihar ta Kebbi na ganin cewa har yanzu akwai gyara ga harakar ilimi a kasar nan musamman jahohin arewacin kasar nan, domin an bar su a baya kan sha’anin tafiyar da harakar ilimi a yankunan arewacin jahohin Arewa maso yamma. Saboda haka masana da suka yi wannan hasashen ga LEADERSHIP A Yau, cewa a sakaye sunayensu, inda suka cewa, “ya zama wajibi ga shuwagabanin jahohin Arewa maso yamma da su mai da hankalinsu ga tabbatar da su gyara harakar ilimi a jahohinsu, domin ilimi shi ne kashin bayan jama’arsu da suke mulki”.

Har ilayu sun ce, “A jihar Kebbi sun san gwamnatin jihar na iya kokarinta wurin  ganin ta inganta harakar ilimi a jihar, amma har yanzu da saura a cikin gyaran da ake yi kan ilimi”.   Saboda haka gwamnatin jihar ta Kebbi ta dubi inda matsalar take, domin yin gyara ga inda ya kamata. Domin indon ka ziyarci makarantar sakandare ta barikin soja watau ‘Army Day Secondary school’ Birnin Kebbi wadda malakar gwamnatin jihar Kebbi ce ka ga irin yadda yanayin ginin makarantar yake, da za ka iya cewa, gwamnatin ba ta kula da makarantu.

Bugu da kari, masana na kira ga gwamnatin jihar Kebbi da kuma duk wata hukumar da ke da ruwa da tsaki kan harkar gudunar da ilimi a jihar ta Kebbi da su yi kokarin ganin cewa sun kai ziyarar ganin da ido a makarantar ta barikin soja domin gyara yanayin ganin azuzuwa da ke cikin makarantar. Daga karshe suna kira ga masu ruwa da tsaki na jihar ta Kebbi da su kai dauke ga makarantar domin ganin cewa an samu nasarar gyara ganin da ya lalace.


Advertisement
Click to comment

labarai