Connect with us

LABARAI

Ya Kamata A Rika Ba Mata Damar Neman Ilimin Zamani –Hajiya Safiya

Published

on


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An yi kira ga masu ruwa da tsaki a cikin al’umma su rika wayar wa da mutane kai kan muhimmancin amfanin ilimin zamani ga mata a zamantakewar al’umma musamman a Arewacin kasar nan. Bbbar Darakta mai kula da manyan makarantun jahar Jigawa, Hajiya Safiya Muhammad ta bayyana hakan a wajen taron tsaffin daliban makarantar ’yan matan Kiru da aka yi a Kano. Ta kara da cewa, ya kamata al’uma da wanda ya sami dama ya yi ilimi ya wayar wa da mutane kai, su san cewa shi fa ilimin zamani ga mata dole ne a neme shi, saboda an ce addini yana tafiya da zamani ne. Wani lokacin wasu kan guje wa ilimin zamani ga mata saboda suna ganin kamar hanya ce ta lalacewa, wanda ba haka ba ne. Ta yi nuni da cewa idan mace ta hada ilimin zamani da na addini za ka ga tarbiyarta da kamalarta ta fi ta wacce ba ta yi ilimin ba. Akwai wuraren da ya kamata a ce mata ne a kan gaba suka hada da koyarwa da fannin lafiya, dan za ka iya kai matarka inda bai kamata ya duba ta ba, shi zai duba ta, wanda a tsari na Musulunci haramun ne.

Hajiya Safiya ta ce idan aka hana mata su yi karatun zamani kullum haka za a cigaba da tafiya a Arewa, wanda ba su dace ba su rika zuwa suna duba mu. Yaushe ne kuma za mu yi wa kanmu fada. Ta ce, akwai dauki da yawa da Gwamnatoci da kungiyoyi ke bayarwa na tallafa wa ilimin mata, amma a Arewa ana samun koma baya sosai. Amma bangaren kudancin kasar nan daga kan malamai, daraktoci, manyan sakatarori yawanci mata ne, amma a Arewa sai ka ga daraktoci mata ba su da yawa.

Hajiya Safiya Muhammad ta kara da kira ga iyaye da al’umma a baiwa ilimin mata muhimmanci. Za a iya magance rashin baiwa ilimin mata kulawa a kan hakan domin Gwamnatoci sun yi nasu kokarin na baiwa mata ilimi kyauta kuma malaman addini ya kamata su rika wayar wa da mutane kai a kan muhimmancin ilimin mata a fannonin da ya cancanci a ce mata suna ciki wannan kuwa nauyi ne da ya hau kan kowa.

Safiya ta yaba wa tsaffin daliban Kiru bisa yin abin da ya kamata saboda sun sami tarbiya da ilimi suka ga yanzu ne ya kamata su fito su ba da gudummuwa dan kwatanta abin da aka yi musu ga ’yan baya.


Advertisement
Click to comment

labarai