Connect with us

LABARAI

Tsohon Shugaban Gidan Rediyon Tarayya Ya Sha Alwashin Inganta Rayuwar Matasan Bauchi Ta Kudu

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Tsohon  Darakta Janaral na gidan rediyon Tarayya Alhaji Ladan Salihu ya ayyana bukatarsa na tsayawa takarar shugabancin Bauchi ta Kudu a majalisar Dattawa ta kasar nan.

Ladan Salihu wanda ya ayyana bukatarsa ta tsayawa tarakar maye gurbin Sanatan Bauchi ta Kudun a shekaran jiya jiya, inda ya mika wa jam’iyyar PDP takardar bukatarsa na tsayawa takarar Sanatan Bauchi ta Kudu da ake shirye-shiryen yi kwanan nan.

Da yake jawabi a wajen mika takardar neman sa’ar, Alhaji Ladan Salihu ya bayyana cewar matasa suna da gagarumar rawar takawa wajen ci gaban al’umma; don haka ne ya bukaci matasa a kasar nan da suke yin amfani da basirarsu domin tabbatar da ci gaban al’umma.

Ladan Salihu ya bayyana matasa a matsayin kashin bayan ci gaban kowace al’umma, ya kuma bayyana cewar zai zage damtse wajen ci gabatar da mazabarsa da zarar jama’a suka zabesa.

Ladan Salihu tun ma da fari, ya fara ne da bayyana kansa wa jam’iyyar da kuma makasudin da ya sabbaba yake neman kujerar, ya kuma shaida wa jam’iyyar asalinsa da kuma tsatsonsa, sai ya bayyana cewar ya fito ne domin kawo gagarumar ci gaba wa wannan mazabar da zarar ya samu Sanatan da ya fito nema.

Da take maraba da dan takarar, shugaban jam’iyyar PDP a shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Sani Ahmad Toro ya sha alwashin cewar jam’iyyarsu za ta yi wa kowani dan takara adalci wajen yin abun da ya dace don baiwa kowa dammar fitowa domin ya fafata neman sa’a.

Toro ya gode wa Ladan Salihu a bisa zabar da ya yi na jam’iyyar a matsayin gidan da zai fito takararsa a karkashin lemarta.

A wani taron gangamin nuna goyonn baya da jama’an unguwar Wunti suka shirya wa Tsohon Darakta Janaral na Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN) Alhaji Ladan Salihu domin nuna masa goyon baya kan bukatarsa ta tsawa takarar Sanatan Bauchi ta Kudu a jiya Lahadi, sun nuna gamsuwarsu gaya da yadda ya fito da kuma kyawawar manufufinsa a kansu.

Kana sun bayyana cewar cancantarsa c eta sanya suka gay a dace su yi masa taro domin nuna masa goyon baya, sun kafa musulai da irin gudunmawar da ya yi ta baiwa jama’an jihar Bauchi a mukaman da ya rike a baya.

Da yake jawabi a wajen taron nuna goyon bayan, Dakta Ladan Salihu ya bayyana cewar zai yi dukkanin mai iyuwa wajen samar wa matasa aiki yi da kuma lalubo hanyoyin inganta rayuwarsu a kowani lokaci da zarar ya samu dammar kasancewa Sanatan Bauchi ta Kudu.

Ta bakinsa, “Za mu yi kokarin samar da aiki yi, domin yanzu da dama matasa babu abun yi, ga ‘yan kasuwa suna son yin kasuwa babu jari, ga masu son tsayuwa da kafarsu amma babu yadda za su yi,” In ji shi.

Ladan ya kara da cewa, “Muna fatan Allah ya bamu zuciyar yin taimako fiye da abun da muka yi a baya, kuma  turbobin da za mu bi wajen kawo ci gaba na rayuwa shine za mu yi kokarin samar da abun yi, domin babu abun yi a tsakanin jama’a,” Ya Shaida.

Kamar yadda ya shaida ya ce wajibi ne a kansu su tashi tsaye domin inganta rayuwar jama’an yankin, “Don haka tilas ne mu tashi mu yi hubbasawarmu domin kawo dukkanin daukin da ya kamata mu kawo wa kanmu domin mu fita daga daga cikin kangin da muke ciki mu kankare wa kanmu kunci da talaucin da ya addabi jama’anmu,”

Ya kuma kara da cewa, “Da yardar Allah za mu ninka abun da muka yi a da dari bisa dadi,”

Daga bisani kuma ya nemi goyon bayan jama’a kama daga iyaye da kuma matasa domin ya samu nasarar kaiwa ga gaci na samun wannan kujerar da ya ke nema na sanatan Bauchi ta Kudu.

Tun da farko matasan unguwar sun ce sun hada taron ne domin su nemasa don ya zo su shaida masa cewar mubayi’arsu tasa ce dari bisa dari, sai suke kirayesa da kada ya mamce da hallarcin da suka yi masa idan Allah ya bashi nasara a zaben da ke tafe na maye gurbin sanatar da ya rasu.


Advertisement
Click to comment

labarai