Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Gano Tare Da Tarwatsa Mabuyar Boko Haram A Borno

Published

on


Daga Bello Hamza

Rundunar sojojin Nijeriya ta bayyana cewa, dakarun “Operation Lafiya Dole” dake ajiya garin Benisheik ta jihar Borno sun gano sansanin horar da dakarunsu.

A wata sanarwar da rundunar ta mika wa manema labarai ranar Litinin wanda Jami’in watsa labaran rundunar “Operation Lafiya Dole” Kanar Onyema Nwachukwu, ya ce, jamiansu sun lallata sansanin gaba daya.

Kanar Nwachukwu ya ce, “ Dakarun mu na rundunar “Troops of Operation Lafiya Dole” dake Beni Sheikh sun gano sansanin horas da dakarun Boko Haram “

“Dakarunmu sun gano sansanin ne a wani wuri da ake kira Alfa a ranar Lahadi da misalin karfe 9 30 na safe bayan da aka samu bayanan surri a kan mabuyar.

“Daga samun bayanan sirrin, jami’an mu suka mamaye illahirin wurin inda aka gudanar da bincike na musamman a lokacin an yi gumurzu da dakarun Boko Haram dake kokarin arcewa daga sansanin, a nan ne aka samu nasarar karbe bindiga daya aka kuma ceto wani mai suna Mallam Abba, wanda aka yi garkuwa da shi a sansanin.

“ Dakarun sojojin mu sun sami nasarar lallata sansanin gaba daya” Inji sanarwar.


Advertisement
Click to comment

labarai