Connect with us

LABARAI

Sama Da Likitoci 4,765 ‘Yan Nijeriya Ke Aiki A Ingila

Published

on


Daga Bello Hamza

Tsohon sakataren kungiyar Commonwealth, Cif Emeka Anyaoku, ya bayyana cewa, fiye da likitodi yan Nijeriya 4,765 ke aiki a kasa Birtaniya a halin yanzu, abin dake nuna sun kai kashi 1.7 na daukacin ma’aikatan kasar Birtaniya gaba daya.

Ya kuma ce, kwararrun likitocin Nijeriya sun yi hijira zuwa kasashen Amurka da Saudi Arabia da Kanada da sauran kasashe a fadin duniya wannda hakan ya kawo mummunan kanfa a sashin lafiya wannan shi ne kuma babban matsalar dake fuakantar sashin samar da kiwon na kasar nan a asibitocin tarayya dana jihohi.

Cif Anyaoku, ya yi wadannan bayanan ne a cikin jawabinsa a wajen bikin cika shekara 110 da kafa asibitin Mission na garin Ogidi a karamar hukumar Idemili North ta jihar Amanbara, an kafa asibitin ne a shekarar 1907.

Cif Anyaoku wanda je rike da mukamin Adazie Obosi, ya ce, Nijeriya ba asarar Naira Biliyan 175 a duk shekara kusan kashi 50 na daukacin abin da gwamnatin tarayya ke ware wa sashin lafiya a cikin kasafin kudin shekara, musamman na wannan shekarar 2018


Advertisement
Click to comment

labarai