Connect with us

LABARAI

Sai Mun Daure Duk Barayin Gwamnati – Osibanjo

Published

on


Daga  Sulaiman Bala Idris

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa za su damke duk wani dan Nijeriya da ya saci kudin gwamnati, sannan su gabatar da shi a gaban kotu don a daure shi.

Mataimakin Shugaban Kasan ya bayyana haka ne a jiya yayin da yake amsa amsoshin tambayoyin daliban makarantar Fimare ta Gwamnati L.E.A dake Gwarinpa a Babban Birnin Tarayya.

Farfesa Yemi Osinbajo ya halarci wannan Firamare ne domin tunawa da ranar hakkin mallaka ta duniya, inda ya je ya karantawa daliban littafi kamar yadda Kungiyar ‘Rainbow Book Club’ ya shirya tare da hadin gwiwar UNESCO. Ya ce, “Duk wadanda suka ginu da cin hanci, za mu kama su, mu kai su kotu sannan a yi kurkuku da su.”

Osinbajo wanda ya karanta wasu jimloli daga littafin, ‘The Legend: Dr. Nnamdi Azikiwe’, ya ayyana cin hanci a matsayin wata hanyar satar kudin jama’a wanda ba hakkin mutum ba.

A ta bakinsa, ya ce, kudaden da barayin Gwamnati ke sacewa sun isa a yi amfani da su wurin gina hanyoyi, makarantu, asibitoci, tashoshin jirgin sama da sauransu.

Ya jaddada cewa mafita ga wannan aika-aika ita ce a gurfanar da dukkan barayin gwamnati ta yadda sauran al’umma za su dau darasi.

A nata jawabin, Shugaban Kungiyar ‘Rainbow Club’, Misis Koko Kalango ta bayyana cewa kungiyar tasu tana horo ne da a ci gaba da karatu domin bunkasar kasa.

Shi ma a nashi jawabi, Darakta Janar na UNESCO, Ms Audrey Azoulay wanda ya samo wakilcin Ifeanyi Ajaegbo ya bayyana cewa ranar 23 ga watan Afrilu aka ayyana a matsayin ranar tunawa da bukin hakkin mallaka na duniya saboda ya zo dai dai da ranar da wasu manyan marubuta adabi biyu suka mutu.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu a nashi jawabin ya yi kira ga wadannan daliban da su kasance nagargaru kuma masu kaunar karance-karance.

Shi ma a nashi jawabin, ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya yabawa Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo bisa karfafawa daliban da yayi wurin horonsu da su kasance ma’abota karatu.


Advertisement
Click to comment

labarai