Connect with us

LABARAI

Rundunar ’Yan Sanda Ta Cafke ’Yan Sara-Suka Goma A Bauchi

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta samu nasarar kamewa gami da tsare wasu ‘yan sara-suka da suka addabi cikin Bauchi da ta’addanci ta hanyan saran jama’a da kuma sukansu.

Bayanin kamen ‘yan sara da sukan ya fito ne daga cikin wata sanarwar manema labaru wacce rundunar ta ‘yan sandan jihar ta aike wa ‘yan jarida jiya 23/4/2018 a Bauchi.

Kakakin Shalkwatan ‘yan sandan jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar shi ne ya sanya hanu kan sanarwar ya bayyana cewar su dai ‘yan sara da sukan sun addabi cikin Bauchi da ta’addanci, wadanda suke tayar wa jama’an jihar da hankula da kuma gudanar da aiyukan da suka jibinci ta’addanci.

Datti ya ce, “A bisa kokarinmu na ganin mun tabbatar da kawar da dukkanin masu dabi’ar sara suka a Bauchi, a makon jiya ne muka samu nasarar kame wasu da muke zarginsu da kasancewa cikin gungun ‘yan sara da sukan,” In ji shi.

Shalkwatan ta bayyana cewar wadanda suka shiga hanunta kan laifin sara da sukan sun hada da Hamza Abdullahi wanda aka fi sani da Mando mai shekarun haihuwa  23, wanda kuma shi ne jagoran gangan ‘yan sara sukan da suka fada tarkon da ‘yan sanda suka dana.

Sauran su ne Tijjani Dahiru 27, Abba Abdullahi wanda ake kira da Dogon Yaro, Muslim Idris,  Ibrahim Musa Ahmed Adam dukkaninsu ‘yan shekaru 20-20 a duniya.

Karashensu din su ne;  Bashir Abubakar 25, Abdulrahman Mohammed 22, Munkaila Mohammed 22 da kuma Umar Hassan wanda ake kiransa da suna Silli na miji ne mai shekaru 23 a duniya.

‘Yan sandan sun bayyana cewar dukkanin matasan da suka shiga hanunsu ‘yan asalin jihar Bauchi wadanda suka rungumi shiga gungun sara da suka.

DSP Kamal Datti ya bayyana cewar makaman da suka kamo matasan da su sun hada da addu’a guda biyar, wata sharbebiyar burki kota, (wuka ke nan), fakej-fakej na kwalin Tramadol mai karfin 225mg da kuma layu, hade da sauran makaman da suka garkamo daga hanunsu.

‘Yan sandan suka ce, dukkanin wadanda suka kama, yanzu haka suna kan gudanar da bincike a kansu, da zarar suka kammala kuma kotu za ta shiga tsakaninsu domin fuskantar shari’a daidai da irin laifin da suka kasance a cikinta.

Rundunar dai ta bayyana cewar hakki ne a kanta a kowani bigire ta kasance mai kare rayuka, lafiya da dukiyar ‘yan jihar.

Don haka ne suka nemi goyon bayan jama’an jihar domin samun nasarar dakile dukkanin wani motsi na ta’addanci don tabbatar da zaman lafiya na ci gaba da habakuwa a jihar.

Rundunar ta kuma nema hadin kai ta fuskacin samar musu da dukkanin bayanai a kowani lokaci.


Advertisement
Click to comment

labarai