Connect with us

LABARAI

Rundunar Sojin Sama Za Ta Yi Noma Don Bunkasa Tattalin Arziki A Bauchi

Published

on


Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A ranar Juma’ar nan ne Rundunar sojojin sama ta Nijeriya mai sansani a jihar Bauci, wato (Nigeria Air Force Base, Bauchi) ta sanar da cewar za ta yi noman shikafa da sauran albarkatun kasa mai fadin kadada (Hekta) 250 domin inganta fannin noma  a albarkatun kasa, don kyautata tattalin arzikinsu. Babban jami’in gudanarwa kuma mai sanya ido da bayar da umurni na sansanin sojin saman da ke Bauci, Air Marshal, Sadik Isma’il Kaita, shi ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da shirin bunkasa aikin noma wanda ya gudana a sansanin da ke Bauci.

Kaita ya nemi gwamnatin jihar ta sake musu wannan fili mai fadin Hekta 250 da ke bayan sansanin na sojin saman domin su samu nasarar gudanar da wannan nomar wacce a cewarsa hakan zai kawo ci gaba sosai. Isma’il Kaita ya bayyana cewar filin da suke neman gwamnatin ta ba su yana bayan ‘NAF Base’ domin su samu nasarar cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na inganta noman shinkafa a karkashin shirin ‘Anchor Borrowers.’

Babban jami’in sojin ya bayyana cewa, sansanin yana son ya kuma samar da albarkatun gona da suka hada da Ayaba, Mongoro, da kuma Gwaiba hade da sauran itatuwa masu fa’ida a kusa da sansanin. Kaita ya bayyana cewa, bullo da shirin noma da suka yi yana daga cikin shirinsu na mara wa gwamnatin tarayya baya ne na bunkasa sashin albarkatun noma da albarkatun kasa a wannan lokacin da gwamnatin ke ta fadi tashin ganin jama’a sun rungumi noma. Ya kuma shaida cewa, alfanun da hakan zai kawo yana da tarin yawa, ciki kuwa har da samar da yanayin da zai rage ma wasu wahalhalun rayuwa a lokacin da suke bakin aikinsu da kuma samar da albarkatun gona cikin sauki. Ya kuma nemi gwamnatin jihar da ta ba su dukkanin goyon baya domin samun nasarar cimma wannan burin da suka sanya a gaba.

Sadik Kaita ya kuma yi amfani da wannan dammar wajen kiran jama’a da su mai da hankali kan tsaron rayukansu da dukiyarsu, la’akari da matsalar da kasar nan take ciki na fuskantar matsalolin tsaro.

Tun da farin, Shugaban sashin gona na sansanin sojin saman da ke Bauci Air Commodore, Useni Sylbanus, ya bayyana cewa, NAF ta kaddamar da wannan shirin ne tun 2016 domin samun zarafin cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya a kan sha’anin gona. Ya bayyana cewa, masu shiga cikin shirin ba tilas a ciki, illa dai kawai domin a samar da hanyar samar da aikin yi don rage matsalar tattalin arziki.

Sylbanus ya bukaci masu shiga shirin da su baiwa sansanin ta kasa NAF hadin kai domin bin dokoki da ka’idojin da aka shimfida. Babban jami’in ya sanar da cewa, jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, da ke Bauci, ta aiko musu da kwararrun jami’an guda biyu kan sha’anin noma domin kula da shirin noma na rundunar, ya kuma kara da cewa suna kuma tsammanin gwamnatin jihar ta Bauci ita ma za ta kara musu yawan adadin masana da za su zo domin duba yanayin aikin da kuma daura masu sha’awar noman a sikeli domin dacewa da nasarorin noma don cin gajiyarsa.

Wakilinmu ya labarto mana cewar ababen da suka wakana a wajen taron sun hada da rarraba takin zamani, sinadaran shuka (iri ke nan) magungunan kashe kwari da sauran ababen da aka raba wa jami’an da suke da sha’awar shiga a dama da su a sashinin noma.


Advertisement
Click to comment

labarai