Connect with us

Uncategorized

Rikicin Duniya!

Published

on


Barazanar tsaro ta hanyar karuwar yake-yake da fadace-fadace a daukacin sassan duniya daga Afirika zuwa Asiya, gabas ta tsakiya zuwa kudancin Amurka, zuwa gabacin turai Magana daya  ce-YAKI kashe-kashe da yake-yake.

A Nijeriya muna fama da kashe-kashen boko Haram na rashin imani, rikicin Ile-Ife inda aka aiwatar da mummunan kisan gilla, zuwa na mayil 12, zuwa Mambila, zuwa Binuwai,Nasarawa,Zamfara, Birnin Gwari da yankunan jihar Neja. Baya ga matsalar ‘yan fashi da makami da masu satar mutane. A janhoriyar Nijar, suna fama da ‘yan Boko Haram, a Kamaru baya ga ‘yan Boko Haram, akwai ‘yan tawayen Ingilishi wadanda ke fafutukar kafa kasarsu. Haka a Chad inda suke fama da ‘yan Boko Haram. A janhoriyar Afirika ta Tsakiya  inda ‘yan Anti Abalaka ke cin naman mutum danye. A Burundi inda shugaban kasar ya aika da mutane da dama barzahu domin ya ci gaba da mulki. Janhoriyar Dimokaradiyyar Kongo nan ma, wani dan mulkin mahadi ka ture ya tura da yawa barzahu don ya ci gaba da mulki. A sabuwar kasar Sudan Ta kudu  yaki ne ake tafkawa na rashin mutunci. A kashe, mata ai masu fyade, kananan yara a tursasa su shiga yaki.Har zuwa yanzu lafiya taki samuwa a Somaliya, ‘yan Al-shabab sun rantse sai sun ga abin da ya ture ma buzu nadi.a Arewacin Mali nan ma rai kwakwai, mutu kwakwai. Libya ta koma Kabari Salamu  Alaikum, inda baya ga yadda ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka, ga kuma matsalar bakin haure wadanda ake kamewa a garkame wurare da dama a gidan kaso. A masar an riga an kafa mulkin kama-karya. An yi ma Mohammed Mursi juyin mulki, aka yanke mai hukuncin kisa, aka murkushe mabiyansa da karfin tuwo. Yanzu haka shugaban kasar Al-sisi ya shirya zaben jeka na yi ka, inda ya sanya hukumar zaben ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

Gabas ta tsakiya, kusan a rikice take, inda Makka ke kai ma Yamalawa hari, an kashe mutane da yawa a Yamel, ciki harda dan lelen Saudiyya Abdullah Sale.A Iran da muna murna an cimma yarjejeniya tsakanin mahunkuntan Tehran da kasashen Yamma game da rikicin nukiliyar kasar, amma zuwan shugaban kasar Amurka Donald Trump, abubuwa sun kare rincabewa. A cikin ‘yan shekarun nan aka tafka yakin ISIL da sauran kasashen duniya. Kungiyar ‘yan  ta;addan  ta halaka dimbin mutane a Irak da Siriya. Rikicin Siriya wanda aka fara tun shekarar 2011 na ci gaba da lakume rayuka. Alkalumma sun nuna an kashe dubban daruruwan mutane a Siriya. Abu mafi muni game da rikicin Siriya shi ne yadda shugaban kasar Bashar Al-Assad yake amfani da makamai masu guba kan mutane. Majalisar dinkin duniya ta haramta amfani da makamai masu guba  amma a rikicin Siriya an maido da amfani da shi. Bashar AlAssad da kasar Rasha sun fara amfani da makamai masu guba kan mutane tun daga shekarar 2013, inda akai ta cacar baki a banza tsakanin Rasha dake goya ma dan kama-karyar baya da kasashen Yammacin Turai da kuma Amerika. Daga Karshe a wancan lokaci an cimma yarjejeniya na cewa Siriya zata amince a kwashe  makaman masu guba a je a zubar. To amma duk da aikin kwashe makaman masu guba da akai a wancan lokaci ya tafi a banza, domin daga wancan lokacin gwamnatin Assad mai samun  goyan bayan Rasha, Iran da Hezbulla sun ci gaba da  yin amfani da makaman masu guba. Na baya-bayan nan shi ne, wanda ya kara tado da cacar bakan, inda shugaban kasar Amurka Donald Trump da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da Firayin Ministan Birtaniya Thresa May, sukai Allah wadarai tare da shan alwashin kai ramuwar gayya.

Gefe guda kasar Rasha ta sha alwashin ci gaba da kare gwamnatin mashaya jinin ta Assad. Abin da ya bada mamaki shi ne, an dauka harin ramuwar da Amerika da Faransa da Birtaniya za su kai ma gwamnatin Assad zai zama wanda zai gurgunta karfin sojar gwamnatin ne, to amma abin sai ya zo ya zama holoko hadarin kaka. Lalle sun harba makamai masu lizzami a wasu wurare da suka ce masu muhimmanci ne, to amma abin bai yi wani tasiri ba. Domin ma maimakon hare-haren su dakushe karfin Assad ,sai ma kara masa kuzari sukai inda  Putin shugaban kasar Rasha da Assad suka fito suna ta surutan banza cewa wai an kai ma kasa mai ‘yanci hari.

Wannan harin banzar da kasashe uku da ake ganin manyan kasashe ne wato Amurka, Faransa da Birtaniya suka kai ma gwamnatin Assad, bai yi wani tasiri ba, sai ma zubar ma kasashen kima da daraja yai a idon duniya.

Kuma abinda wannan ke nunawa shi ne Bashar Al’assad zai ci gaba da cin Karen shi babu babbaka, Rasha da kasar Iran za su ci gaba da kashe duk  wani dan Siriya day a fito y ace bai amince da mulkin mulkiyar iyalan gidan Assad ba.

Akwai yiwuyar Siriya ta kara amfani da makami masu guba sosai akan ‘yan tawaye da fararen hula.

A yayin da ake cikin wannan tashin hankali da rikice-rikice, za a ga kasawar majalisar dinkin duniya. A duk lokacin aka kai batun a kwamitin Sulhu, to kasashen duniya suna rabuwa ne gida biyu, inda Caina, Rasha da sauran ‘yan kwamunis kamar Koriya ta Arewa ke hade kawunansu su lalata abin idan har bai masu dadi ba. Kazalika suma kasashen yamma da Amurka sukan bijire ma duk wani ra’ayi da kasar Rasha ta bijiro da s hi.Muna ganin a haka, to duniya ba za ta taba zaunawa lafiya ba.A wannan karnin na 21 muka ga yadda kasar Rasha ta mamaye yankin Kirimiya na Kasar Ukraine, kuma har yau babu abin day a faru. Ko shakka babu Rasha tana taka muhimmiyar rawa wajen hargitse duniya, karan tsaye ga Dimokaradiyya da kokarin maido da mulkin gurguzu na kama-karya a duniya. Dubi zargin katsi-Landan da ake ma Rasha a zaben kasar Amurka? Dubi yadda ake zargin Rasha tai amfani da makamai masu guba akan tsohon dan , asirinta a London, dubi yadda Rasha ke kutse a kwamfutocin kasashen duniya domin leken asiri ko satar fasaha. Duk wannan na nuna take-taken Rasha na maida hannun agogo baya game da samar da lumana, sulhu da zaman lafiya a duniya.

Yanzu dai za mu ce duniya na cikin hadari, domin majalisar dinkin duniya ta zama majalisar Rasha da manyan kasashen Yamma wadanda bas u damu da yadda shugabannin kama-karya da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke ci gaba da kisan mutane babu gaira babu dalili.Allah ya kawo mana sauki.


Advertisement
Click to comment

labarai