Connect with us

LABARAI

Majalisa Na Iya Zama Ko Ba Sandar Majalisar –Lauyoyi

Published

on


Daga Umar A Hunkuyi

Lauyan nan mai rajin kare hakkin dan adam, Mista Femi Falana, ya fada a ranar Lahadi cewa, harin da wasu batagari suka kai Majalisar Dattawa, inda kuma suka yi awon gaba da sandar Majalisar da kuma rigingimun da suka biyo bayan faruwar lamarin, sam ba su dace ba. Inda ya ce, ba inda a tsarin mulki aka ce sai da sandan ne Majalisun ya halasta su zauna.

Falana, ya bayyana hakan ne wajen kaddamar da sabon mutum-mutumi mai tsawon kafa 44 na Gani Fawehinmi, a wurin shakatawa na Ojota, Legas, wanda gwamnatin Jihar Legas din ta gina, domin murnar ranar haihuwan mamacin ta 80.

Ya yi nu ni da cewa, abin takaicin da ya faru a Majalisar kwanan nan sam bai kamata ba, domin kuwa Majalisar ba ta bukatar sandan kafin ta zauna ta zartar da duk wani lamari.

Babban Lauyan ya ce, “Ga ‘yan majalisun da ke Abuja, Gani Fawehinmi, zai gargadi masu yin fada ne a kan sanda. Na yi farin ciki da kasantuwar lauyoyi masu yawa a nan, hatta babban mai shari’a na Jihar Legas yana wannan wajan. Babu inda tsarin mulkin Nijeriya ya ce, sai da sandan Majalisa za ta zauna. akwai kuwa sassa 320 cikin kundin tsarin mulkin, amma ba inda aka yi nu ni da sanda.

“To me zai sa su tsaya suna fada kan abin da tsarin mulki bai san da shi ba? Ba gaskiya ne ba, cewa sai da sandan ne Majalisa za ta yi aiki. Wannan al’adar Ingila ne kawai. Mu ka aro,muke kuma fada a kanta,” in ji Falana.

Ya kuma karfafa cewa, wasu tituna da mahimman wuraren da aka sanya masu sunayen wadanda ya kira da azzalumai irin su, Lugard, Bourdillon, Kingsway, Lebentis, James Robertson, da sauran su, ya kamata a hanzarta canza su da mutanan kirki na nan cikin gida, ya kwatanta da shugabannin na mulkin mallaka, da cewa, shuganannin zalunci ne,’ wadanda a cewar sa, yawancin su duk manyan dillalan cinikin bayi ne da suka kuma sace mana albarkatun kasarmu.

Falana, ya bayyana halayen kwarai na marigayi Gani, wanda ya bayyana shi a matsayin fitacce abin koyi wanda ya tsayawa gaskiya, rikon amana da kuma aikata gaskiya a hukumance, kuma kaya a jikin azzalumai.

Falana, ya yabawa gwamnatin Jihar Legas kan gina mutum-mutumin mai tsawon kafa 34 da ta yi, a bisa bigire mai tsawon taku 10, wanda hakan ya mai she shi wani babban abin sha’awa a wurin shakatawan na Ojota.

“Gwamnatin Jihar Legas ta yanke shawarar girmama mutanan da suka yi wa al’umma aiki ne, ba kamar wani gwamna ba, wanda ya girmama wani watanni shida da suka shige, sai muke gargadin sa da ya karya mutum-mutumin da ya yi na mutumin domin azzalumi ne yake girmamawa. A yanzun haka, wannan shugaban da yake girmamawan a Owerri, Jihar Imo, yana can yana fuskatar shari’a a Afrika ta kudu.

“Ina kira ga gwamnatin Jihar Legas da ta canza sunayen dukkanin tituna da wuraren da aka sanyawa sunayen azzalumai, musamman shugabannin turawan mulkin mallaka, wadanda suka zo kasarnan suka kwashe mana albarkatunmu. Ya wajaba mu hanzarta goge sunayen wadannan wuraren. Wasu daga cikin su akwai, Bourdillon, Kingsway da makamantan su. Abin kunya ne a ce har yanzun gwamnatinmu tana girmama wadannan azzaluman, da yawan su duk dillalan bayi ne. amma har yanzun a ce wai kuma muna biyan su kudaden Fensho.

“Gani ya tsayawa gaskiya ne, da rikon amana da kuma gudanar da gwamnati a bisa turba ta gaskiya, sai ya kasance kaya cikin jikin azzalumai.

“Ya rayu ne a wani lokacin da hadari ne ga duk wani mai fafutukar kare hakkin dan adam ya iya tsayin daka a kasarnan. Amma sai ya cire tsoro, sai ya kasance azzalumai su na tsoron sa.

“A lokacin mulkin Soja, sa’ilin da duk aka daure mu, na same shi mai dagewa sosai kan neman canji, watau canji daga talauci zuwa rayuwa mai dadi ga talakawa.

“Yanzun ya ta fi, amma tamkar yana raye ne, saboda mutanan kwarai ai ba sa mutuwa, domin har abada sakon su ba ya karewa. Lokacin da wancan mutum-mutumin na shi ya ruguje muna ta mamaki, amma wannan na yanzun akwai tabbacin nagartan sa har tsawon zamani,” in ji Falana.

Ya kara da cewa, babban yakin da Gani ya fuskanta, wanda har ya kusa yin sanadiyyar rayuwarsa shi ne, fafutukar sa na nemo mutanan da suka kashe Dele Giwa.

A cewar sa, abin da bai kai da cimma nasarar sa ba kenan har lokacin mutuwarsa, amma ya ji dadin hakan da ya yi, domin a sanadiyyar hakan duk wanda aka kashe a Jihar Legas, bisa zalunci, ba kawai ana sallaman wanda ya yi kisan ne ba, ana ma gurfanar da shi a gaban hukuma.

“Gwamnatin Jihar Legas ta kafa wata doka, wacce take tabbatar da duk wanda aka kashe a Legas, to tabbaci hakika sai an gano wanda ya kashe shi. Wannan yaki ne da bai yi nasarar sa ba lokacin da yake raye sai a bayan mutuwarsa,” in ji Falana.


Advertisement
Click to comment

labarai