Connect with us

LABARAI

Kage: Iyalan Dansadau Za Su Kai Gwamnatin Zamfara Kotu

Published

on


Daga  Sulaiman Bala Idris

A jiya ne Iyalan Sanata Sa’idu Dansadau suka yi barazanar maka gwamnatin Jihar Zamfara a kotu matukar wa’adin kwanaki 14 suka cika ba tare da gwamnatin ta janye kagen da ta wallafa a kafafen watsa labarai ba.

Wannan wa’adi na kwanaki 14 daga Iyalan Sanata Sa’idu Dansadau na kumshe ne a wata takardar da lauyan Iyalin Sanatan, Chinedum Odenyi ya aikewa Gwamnatin Zamfara.

Haka kuma takardar ta yi nuni da cewa, Iyalin Sanata Dansadau din sun fitar da wannan wa’adin ne bisa jagorancin dansa Abubakar Saidu Dansadau a madadin daukacin Iyalai.

Wa’adin nasu ya biyo bayan wata takarda da gwamnatin jihar Zamfara ta watsa mai taken; “SENATOR SAIDU DANSADAU: A POLITICIAN OR A CONFLICT ENTREPRENEUR?”, wacce kuma ta ke dauke das a hannun mai ba gwamnan jihar Zamfara shawara akan kafafen watsa labarai, Ibrahim Dosara.

Takardar wa’adin ta kara da cewa; “A wannan talla da ku ka wallafa, gwamnatinku ta yi wa mahaifinsu kage, Sanata Dansadau sakamakon hirar da ya yi da kafar sadarwa ta BBC Hausa dangane da abin da ya fahimta a matsayin gazawar jami’an tsaro a lamarin kashe-kashen dake afkuwa a Zamfara.

“A wannan kage, gwamnatin Zamfara ta fadi kalamai na cin mutunci ga mahaifinsu, wanda ya taba kimarsa a idon al’umma. Lamarin da matukar ba a nemin afuwansa ba, zai ci gaba da taba mutuncin mahaifinsu da iyalansa.” inji takardar wa’adin.

Takardar wa’adin ta ci gaba da bayyana cewa; “mafi muni daga takardar kagen da gwamnatin Jihar Zamfara ta fitar shi ne wurin da take cewa: Domin wadanda ba su san me ke faruwa ba, su fahimci cewa Sanata Dansadau ya kaddamar da kamfen din batanci ne ga Gwamna YAri saboda ‘yar tsamar da yake da ita akan gwamnan. Kuma wannan ‘yar tsama ta samo asali ne tun bayan da Gwamnan ya tumbuke shi daga shugabancin Kwamitin bibiya da biyan Kwangilolin da gwamnati ta bayar. Tun daga sannan ya bijiro da farfagandar batanci ga gwamna Yari don kawai ya cire shi daga kwamiti.

“Sai dai wannan kalamai na gwamnatin Zamfara ba komi bane face murguda zance da kage. A dalilin haka ne Iyalan Sanata Dansadau suke son tunatar da Gwamnatin Zamfara cewa, Mahaifinsu ba wai an tumbuke shi bane daga shugabancin wannan kwamiti, aikin da ya amsa da kyakkyawar niyyar taimakawa Gwamnan a daidai lokacin da gwamnatinsa ke bukatar taimako. A kashin kansa Sanatan ya rubuta takardar Murabus a ranar 11 ga watan Nuwambar 2013, wacce ya aike wa Mai girma GWamnan Jihar Zamfara.

“Sannan kuma Gwamnan ai yana iya tunawa cewa, da kansa ya rattabawa takardar godiyar da gwamnatin ta rubuto hannu wacce ke dauke da kwanan wata 10 ga watan Disambar 2013, mai dauke da lamba GHG/ZM/002/BOL.1, wacce a cikinta ka nuna farin ciki da jin dadi dangane da irin gudummawar da Sanata Dansadau ya bayar”. inji takardar wa’adin


Advertisement
Click to comment

labarai