Connect with us

LABARAI

Iyayen ’Yan Matan Chibok Sun Yi Mummunan Hatsari

Published

on


Daga Bello Hamza

Wasu iyayen ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace sun yi munmunar hatsari a kan hanyar Song zuwa Yola ta jihar Adamawa ake Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Sakamakon hatsarin, mutum daya ya riga mu gidan gaskiya yayin da mutum 17 suka ji raunuka, hatsarin dai ya auku ne ranar Lahadi.

Majiyarmu ya nuna cewa, iyayen suna kan hanyarsu ne zuwa taron iyaye da malamai (PTA) na American Unibersity of Nigeria (AUN) Academy Yola yayin da hatsarin ya auku.

Duk da cewar har yanzu hukuman yansanda basu tabbatar da faruwar hatsarin ba, amma jami’in watsa labaran kungiyar Mista Ayuba Alamson ya yi bayanin ainihin abin daya faru.

“Suna kan hanyar su ne ta kai wa yaranmu ziyara tare da halartar taron PTA na AUN. A dai dai karfe 10.00 na safe hatsarin ya rutsa dasu a garin Song.

“Ana gyaran hanya ne saboda haka wasu motoci na yin zagaye ana cikin haka ne mota ta kubce wa wani inda ya yi gaba da gaba da wata  babbar motar dake aikin gyaran hanyar”

“A nan take Yakubu Yerima ya rasu yayin da mutum 17 suka ji mummunan raunuka” a jawabin day a yi ta wayar hannu.

Mista Alamson ya kuma kara da cewa, “Abin nada tayar da hankali, muna ta rasa iyayen ‘yan matan Chibok zuwa yanzu iyane 20 sun rasu, bama fatan rasa wani a halin yanzu.’’

Da yake yi wa iyayen ‘yan matan Chibok ta shafinsa na Twiter, mai makarantar kuma tsohon mataimakin shugababn kasa, Atiku Abubakar,ya ce, “Na yi matukar bakin ciki da ji cewa, iayyen ‘yan matan Chibok dake karatu a AUN Academy” sun gamu da mummunan hatsari har mutum daya  ya mutu wasu kuma sun ji raunuka, ina mai addu’ar Allah ya jikansu da rahama” inji shi.

‘Yan Boko haram ne dai suka sace ‘yan matan makarantar Chibok ne a shekarar 2014 a dai dai lokacin da suke shirin yin jarabawa. Sace su ya jawo cecekuce a fadin duniya an kuma yi yakinin cewa, sace su ya taimaka wa jam’iyyar adawa na APC kawar da shugaba Goodluck Jonathan daga mulki a shekarar 2015.

Wasu daga ciki ‘yan matan da aka ceto suna karatu a makaratar AUN a bisa tallafin gwamnatin tarayya, fiye ‘yan mata 100 ne kuma ke a hannun ‘yan ta’adda har zuwa yanzu.


Advertisement
Click to comment

labarai