Connect with us

LABARAI

Gwanman Jihar Kano Na Tallafa wa Harkar Ilimi A Fadin Jihar

Published

on


Daga Hussain Suleiman

An bayyana cewa, gwamman jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje na bakin kokarinsa wajen bai wa hakar ilimi kulawar da ya kamata a daukacin kananan hukumomin jihar guda 44 idan aka kwatanta da shekarun baya. Wannan bayani ya fito ne daga bakin sakataren ilimi na karamar hukumar Gwale, da ke jihar Kano, Malam Mahmud Muktar a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya a garin Kano. Malam Mahmud Muttar ya ba da misali da karamar hukumar ta Gwale inda gwamnatin ta jihar Kano ta raba littafan karatu da na rubutu a daukacin makarantun karamar hukumar.

Karamar hukumar ta Gwale ta amfana da littafan karatu da na rubutu da adadinsu ya kai kimanin 5,000 nan take kuma aka rarraba su. Bayan haka kuma an raba kujerun zaman dalibai ga wasu manyan makarantu 28, abin farin ciki gwamnatin ta Ganduje ta yi wa malaman jihar karin

girma har su kimanin 40,000, malaman da ke koyarwa a kananan hukumomi sun amfana da karin girman. Inji sakataren ilimi na Gwale.

Shugaban karamar hukumar Gwale shi ma na bakin kokarinsa domin ganin ilimi ya inganta, inda ya zuwa yanzu ya fara aikace-aikace ga wasu makarantu uku da ke karkashin kulawarsa, sannan ya kuma sanya na’ura mai kwakwalwa a ofishin kula da harkar ilimi da ke yankin. Yakan kuma kai ziyara lokaci-lokaci domin ganin yadda harkokin ilimi da koyarwa ke tafiya da kuma malamai saboda haka babu abin da za su cewa shugaban karamar hukumar sai godiya.

Mahmud ya yi amfani da wannan dama inda ya yi kira ga malamai masu koyarwa a makarantun jihar Kano da kasa baki daya da cewa su kara kaimi wajen koyar da dalibai da kuma ganin harkokin ilimi sun kara inganta . Wannan na daya daga cikin kusan kullum kafin ya shiga ofis sai ya kai ziyara wasu makarantu dake karkashin kulawarsa domin sanin halin da suke ciki. Yana kuma taimaka wa duk malamin da ya yi hazaka wajen mayar da hankali musamman karramawa. Yakan kuma dauki mataki ga duk malamin da ya yi wasa ko kuma sakaci a kan koyar da dalibai. Daga karshe ya ce, babban burinsa shi ne ya ga karamar hukumar Gwale ta yi fice a kan ilimi a fadin jihar Kano, Gwamnan jihar Kano shi ma abin a mara ma shi baya ne domin ya ci gaba da aikace- aikace da yake yi wa al’ummar jihar.


Advertisement
Click to comment

labarai