Connect with us

WASANNI

An Shawarci Salah Daya Koma Real Madrid Ko Barcelona Idan Sun Neme Shi

Published

on


Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham da kasar Masar, Ahmad Mido, ya ce yakamata Muhammad Salah yabar Liberpool idan kungiyoyin Barcelona ko Real Madrid suka nemi daya koma kasar Sipaniya da buga wasa.

Muhammad Salah, mai shekara 25 a duniya dai shine ya lashe kyautar dan wasan dayafi kowanne dan wasa kwarewa a gasar firimiyar wannan shekarar bayan daya doke dan wasan Manchester City, Kebin De Bruyne sannan kuma ya zura kwallaye 41 a raga a wannan kakar a dukkan wasannin daya buga a kungiyar tasa.

Sai dai Mido, wanda ya taba bugawa kungiyar Tottenham da Celta Bigo ta kasar Faransa wasa yace idan har daya daga cikin wadannan kungiyoyin suka nemeshi kawai yatafi saboda idan yaje kokarinsa zaifi haka.

Mido yaci gaba da cewa shima ya taba zaman kasar ta Sipaniya kuma yadda Real Madrid take fama da rashin kokarin Bale da Benzema idan yakoma kungiyar zai samu dama sosai yadda yakamata.

Ya kara da cewa gasar laliga tanada sauki ba kamar firimiya ba kuma zai samu yan wasan da zasu taimaka masa a can sai dai yace duk da haka baya nufin Liberpool ba babbar kungiya bace kuma dan wasan ya cancanta daya zauna a kungiyar.

Sai dai abune mai wahala Liberpool ta amince da rabuwa da dan wasan nata wanda ta siyo daga Roma ta kasar Italiya akan kudi fam miliyan 36 a watan Yulin shekarar data gabata.

A yanzu dai dan wasan shine yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a gasar firimiya bayan daya zura kwallaye 31 kawo yanzu kuma saura wasanni 4 a kammala gasar.

                                                                      


Advertisement
Click to comment

labarai