Connect with us

LABARAI

An Bukaci ’Yan Nijeriya Su Guji Gurbata Kasa Da Leda

Published

on


Daga Bello Hamza

Gwamnatin tarayya ta bukaci yan Nijeriya dasu dauki matakan da zai kawo karshen gurbatar muhalli da ake yi da leda, ta yadda zamu kare duniyar mu.

Karamin ministan muhalli, Mista Ibrahim Jibril, me ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwar daya gabatar a garin Abuja,jami’ar watsa labaransa Misis Esther Agbarakwe, ce sanya wa sanarwar hannu, a cikin bikin wannan shekarar na “2018 World Earth Day”.

Rahotannin sun nuna cewa, ana bikin ranar nahiyar duniya ce duk ranar 22 ga watan Afirilu, taken bikin na wannan shekarar kuma shi ne, yekuwar kawo karshen mamayar leda a muhallinmu “End Plastic Pollution.”

“Ana bukatar yan Nijeriya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin aiyukan da zasu kawo karshen gurbacewar muhalli da leda ke kawo wa.

“Leda na gurbata teku da halittun dake ciki hakan kuma yana cutar da rayuwar mu gaba daya “ Inji shi.

Ta kasa da cewa, gwamnati na duba yiwuwar hana amfani da leda gaba daya tare da samar da wani hanyar da za a rinka amfani wajen kulle kayan abinci da sauransu.

“Muna karfafa mutane wajen su rinka sake amfani da leda maimakon zubarwa, wannan wani gudummawa ce da ake bukatar kowa ya bayar da musamman kuma gwamnatoci a dukkan matakai”

“Har sai mun dauki wadannan matakan warware matsalar ba zai yi sauki ba, matsalar zai wuyar tafiya Inji Dakta Cristiana Paşca Palmer, sakatariyar kungiyar majalisar dinkin duniya mai kula da halittun na “Biological Dibersity” a sakon da ta gabatar.

“A shekarar 1950, yawan alumma duniya yana mutum Biliyan 2.5 ana kuma samar da gurbataccen leda har Tan Miliyan 1.5. Haka kuma a shekarar 2016, yawan Mutanen duniya yana fiye da mutum Biliyan 7 ana kuma samar da gubataccen leda har Tan Miliyan 300” Inji Ministan.

Ya kara da cewa, gurbacewar muhalli da leda ke yi wani babban matsala ne da ake fuskanta.

“Muna iya ganin leda ana yawo a rafukan mu da kogi da teku gaba daya, leda na bata muhalli hakan kuma ba shafar lafiya mu dana miliyoyin yaran mu da matakan gaba daya”.

“Dukkan mu nada hannu a wannan matsalar, a wasu lokutta bana sane da abin da muke yi yana haifar da matsala, dole kuma mu hada hannu don kawo karshe matsalar gaba dayanmu” Inji Baleria Merino, mataimakiyar shugaban kungiyar “Global Earth Day at Earth Day Network.”

Mista Jibril ya kuma kara bayyana cewa, ma’aikatan muhalli tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki sun fito da wani tsari don ganin bayan leda da dangin ta masu gurbata muhalli.

Ya ce, a halin yanzu ana shirin fito da dokan kasa a kan yadda za a sarrafa leda don kaucewa bata muhalli daya keyi.

Ya ce, gwamnati na kuma shirin aiwatar da tsarin “National Plastic Waste Recycling Programme” da samar da ma’aikatan sarrafa leda tare da hadin gwiwar Kanfanonin masu zaman kansu tare kuma da gwamnaticin jihohi.

“Tuni aka kafa wurin sarrafa ladan har guda 18 ana kuma gab da kammala sauran wuraren.

“Tuni aka fara aiki a na garin Ilori dana Lakwajja ana kuma gab da fara aiki a wanda yake a garin Karu ta karamar Karu a jihar Nasarawa.

“Wasu wuraren sun hada da Bola Jari a jihar Gombe da kuma Leda Jari a jihar  Kano ” Inji Ministan.


Advertisement
Click to comment

labarai