Connect with us

LABARAI

Abubuwan Da Suka Yi Mana Maraba

Published

on


Ziyarar aikinmu a Kasar Sin za a yi cewa tubalinta ya fara ginuwa ne tun daga Babban Birnin Tarayya Abuja, kasancewar jagoran da aka hada mu da shi a tawagarmu daga ofishin jakadancin Sin na Nijeriya, Mista Lian ya fara yi mana muhimman bayanan da ya kamata mu sani game da yanayin kasar ana saura jibi za mu tashi.

Ya nunar mana da cewa da safe ana samun sanyi sama-sama ba mai tsanani ba a can, don haka yana da kyau mu yi tanadin sutura mai dan kauri da za mu sanya idan za mu fita da safe, da maraice kuma za mu iya sa tufafi mara kauri domin a wannan lokacin gari ya sarara. Jagoran ya kuma tambayi irin abincin da muka fi so tun daga kalaci zuwa abincin dare. Kowa a cikin tawagar ya bayyana abin da ya fi kwanta ma sa a rai na abinci. Ni dai mai rubuta wannan rahoton, na ce ba na son abinci mai yaji.

Dai-dai misalin karfe uku na rana jirginmu ya tashi daga Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikwe zuwa Adis Ababa, Babban Birnin Kasar Habasha domin yada zango. Mun sauka a tasha lokacin sallar isha’i, bayan mun yi sallah sai Mista Lian ya kai mu wani shagon sayar da abinci domin cin abincin dare. Tun daga wannan shagon na san cewa mun fara jin kamshin Kasar Sin, kasancewar shagon na mutanen kasar ne kuma irin abincin kasar ake saidawa; koda yake akwai wasu Habashawa da na gani suna aiki a shagon.

Jirginmu ya tashi daga Adis Ababa karfe goma sha daya na dare da ‘yan mintina, ni dai jim kadan bayan keta hazo barci ya yi awon-gaba da ni wanda farkawa na yi kawai na ga rana, ban san lokacin da gari ya waye ba har ranar ta fito. Mun sauka Babban Filin Jiragen Sama na Pudong da ke Birnin Shanghai da rana, sai dai ban san ko karfe nawa ba ne, kasancewar agogon wayata ya ki sauyawa daga lokacin Adis Ababa zuwa na Kasar Sin.

Wani abu da na fara lura da shi game da Kasar Sin shi ne, suna da matukar kula a kan batun sha’anin kiwon lafiya da kuma tsaro, sakamakon irin sanarwar da aka yi ta yi wa fasinjojin jirginmu kan yadda za a duba lafiyarsu da fasfo da sauran bayanansu a filin jirgin kafin kowa ya nufi yankin da zai je.

Da yake filin jirgin Shanghai yana da matukar girma, akwai jirage masu yawa manya da kanana, kana ga ma’aikata kowa ya kasa-ya-tsare a kan aikinsa babu wasa. Mota ta kwashe mu zuwa wurin binciken fasinja. Hakika harabar ginin da muka shiga ta kai matsayin kyau a ko ina cikin duniya. An kawata ta da fitilu masu haske wandanda haskensu yake daukar ido saboda daben zamani  da sauran kayan karau da aka kawata ciki da su.

Ba mu bata lokaci ba sosai wajen binciken jami’ai daban-daban na kasar tun daga kan masu kula da shige da fice har zuwa kwastan, saboda muna tare da Mista Lian daga ofishin jakadancin kasar na Nijeriya. Idan za a iya cewa mun bata lokaci, to bai wuce wurin jiran kayan da muka taho da su ba. Mun dan jima kafin mu ga kayan saboda yawan kayan da aka yi dakonsu a lokacin, da muka tashi gani kuma kusan a lokaci daya kowa daga cikin ‘yan tawagarmu ya ga nashi. Bayan wasu ‘yan mintina kalilan, wani jami’i da yake aikin jagoranci ga baki, Mista Charles ya zo ya tarbe mu muka nufi tashar jirgin kasa.

Jirgin na mayen karfe ne wanda aka gina tasharsa a jikin Filin Jiragen Sama na Shanghai. Yana da wani irin sauri na musamman, domin kamar yadda jagororin namu suka yi mana bayani, yana gudun kilomita 430 a cikin awaya daya. Wato kamar misali a Nijeriya, jirgin zai iya zuwa Sakkwato daga Kaduna a cikin awa daya. Hakika irin wannan jirgin muke bukata a Nijeriya musamman saboda yanayinmu ko in ce dabi’unmu na shan-yanzu-maganin-yanzu. Kwata-kwata tafiyar minti bakwai muka yi daga Filin Jirgin Saman Pudong zuwa titin mota na Long Yang, an ma ce da jirgin ya kara sauri za mu iya zuwa a cikin minti hudu rak!.

Bayan mun sauka mun tsaya jiran direban da zai kai mu masauki, hira ta hada mu da Mista Charles inda ya nuna mun wasu motoci masu amfani da lantarki. Sam motocin ba su da kara ballantana su cika gari da hayaniya irin namu. Kuma wadanda ma ba na lantarkin ba, su ma ba su da hayaniya, illa kawai idan mutum ya zo tsallaka titi ya duba da kyau kar ya dogara da karar gunji.

Akwai masu hawa babura sosai kuma su ma baburan nasu ba su da gunji ballantana cika mutane da hayaki.

Direban mu ya zo a wata doguwar babbar motar bus, muka shiga aka nausa da mu masauki a otel din Sheraton. A lokacin magriba ta riga ta yi, kuma ga gajiyar tafiya, don haka aka yanke shawarar mu soke ziyarar da za mu kai zuwa Kogin Huangpu zuwa gobe. Kowa ya shiga masaukinsa ya kintsa, aka kira mu zuwa cin abincin dare, bayan mun kamala muka yi wa juna asuba tagari tare da kulla niyyar sammako zuwa tashar dakon jiragen ruwa da aka gina a tsakiyar teku ta Yangshan wadda ita ce lamba ta daya a duniya.

A biyo mu gobe, idan Allah ya kai mu domin jin yadda tashar take da kuma hanyar mota mai matukar ban al’ajabi da aka gina daga kan tudu da ta keta tsakiyar teku zuwa tashar.


Advertisement
Click to comment

labarai