Connect with us

RAHOTANNI

Ya Kamata Matasa Mu Yunkuri Don Kare Martaban Mu -Abdulmalik

Published

on


Dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar PDM a jihar Neja, Alhaji Sa’idu Abdulmalik ya bayyana cewar takararsa na da nasaba da kudurinsa na ceto tattalin arzikin jihar daga durkushewa. Ya ce saboda sakaci da rashin sanin makaman mulki yasa da daman wadanda ke samun damar dafe madafun iko ba sa iya aiwatar da komai na cigaba.

Ya ce ko babu kason da gwamnatin tarayya ke baiwa jahohi, Neja na da hanyoyin da za ta haddaka kan ta. Ya kamata matasa mu farga daga  nisan da aka yi mana wanda kan hakan ne yasa a kullun ake kiran mu ‘yan maula, muna da arzikin da zamu gina jihar nan ta hanyar kirkiro ayyuka ga jama’a wanda hakan zai rage mana radadin rashin aiki da ke damun matasan mu.

Alhaji Sa’idu ya ce na fito takarar kujerar gwamnan Neja a inuwar PDM kuma da yardar Allah zan kaddamar da takara ta da zaran hukumar zabe ta bada daman hakan.

Ba zamu zauna muna tura mortar masu Ido da kwalli ba, da zaran sun samu nasara su koma suna zargin mu. Idan ka yi magana akan matasa na yawon maula, wani shiri kayi na raba su da maulan, jihar nan muna da arzikin da kowa zai dara, amma rashin tsari da tunanin zaunawa dukiyar jama’a yasa an hana mu cin moriyarta.

Ba zamu gushe ba, zamu jagoranci matasa akan takarar kowani irin mukamin siyasa a kasar nan, mu ne muka san ciwon junan mu, mune muka san abinda ya kama ce mu, ku bar mana dukiyarmu in har kuna son mu daina zuwa kofar gidajen ku. Bai kamata giyar mulki ta rika jagorantar masu mulki suna walakanta talakawan ba.

Mun hango haske a gaban mu, shi yasa muka rungume PDM, mun fahimci tsare-tsarenta na mutunta jama’a, na gina kasa ne, na amana ne don haka ba za mu ja baya ba zamu tsaya tsayin daka don kwato ‘yancin mu.


Advertisement
Click to comment

labarai