Connect with us

LABARAI

Nijeriya Na Cikin ani Mawuyacin Hali –Gwamnan Bayelsa

Published

on


Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya ce, Nijeriya na fuskantar zub da jini da rikice-rikice da rarrabuwa fiye duk wani lokaci a tarihinta baya.

Ya ce, kashe-kashen da ake zargin makiyaya ke a fadin kasar nan wani alami ne na rugujewar kasar nan, gwamnan ya bukaci a kara kaimi wajen dukufa domin yin addu’a da fatan Allah ya bamu ikon tsallake wannan matsalar.

A wata sanarwa da jam’in watsa labaran Gwamna Dickson, Francis Agbo ya sanya wa hannu,ya nuna cewar, gwamnan ya bayyana haka ne a yayin gudanar da taron add’ua na kasa da kungiyar Kiristoci na Yenagoa suka jagoranta. Ya ce, dole ‘yan Nijeriya su hada kansu ta hanyar addu’a da aiki gare cikin adalci tare da fuskantar kowa a matsayin dan kasa mai hakki daya.

Gwamnan ya yi korafin cewa, a nan zubar da jinni a kasar nan fiye da kima ya kuma bukaci shugabannin kasa dasu dauki nauyin alhakin tsayar da zubar da jinin dake faruwaa fadin kasa. Ya kuma ce fitowar wannna kungita ta Nijeriya Prays a daidai wannnan lokaci abu ne mai mahimanci domin hakan zai karfafa dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ko darikarsu basu  rungumi a kidar yi wa kasa addu’a a ko wanne lokaci.

Ya ce, “A wannan kasar, ana kashe bayin Allah ba tare da la’akari wani addini suke yi ba, ana yanka sub a tare nuna imani ba, ana matuwar zubar da jinni a kasar mu, dole mu hada kanmu mu yi addu’ar Allah Ya ceto kasar mu, mu kuma yi abin daya kamata”

Allah Ya hadamu a matsayin mutane da yan kasa daya saboda haka dole a yi maganin rashin adalci a ko Ina a fadin kasa dole kowa ya damu da faruwar rashin adalci a ina fadin Nijeriya. Ina mai haduwa daku da fatan Allah Ya kawo karshen kashe kashe nan da sunan Allah. Allah Ya kawo mana dauki ta yadda mutane zasu fahinci bukatar yin adalci da abin daya kamata ga danuwan ka dan adam.

“Duk wani daya ki yi wa wani mutum adalci to shima ya rasa wa kansa adalci gaba daya. Saboda Allah Ya halicce mu da haskensa ne don mu yi kyakyawan aiki tare da adalci ga kowa. Mu kuma yi fatan samun kasar da duk dan Nijeriya zai yi alfaharin kiran kansa dan Nijeriya.

A nasa Jawabin tun da farko, Nigeria Prays, Yakubu Gowon, ya mika godiyarsa ga gwamna Seriake Dickson a daman daya basu suka gudanar da taron adduar a dakin taro na Ecumenical Centre, ya kuma yaba wa irin katafaren ginin da aka yi na dakin taron. Ya kuma bukaci sauran Gwamnonin kasar nan su yi koyi da gwamnan Dickson na irin wannan dakin taron addua a jihohinsu saboda samun albarkar Allah madaukakin Sarki

Tsohon shugaban mulkin sojan ya kuma lura cewar addua Nada karfin warware matsalolin kasar nan fiye da yadda janarorin soja da sojoji zasu iya yi da kayan yaki, ya kuma tabbatar wa yan Nijeriya cewa Allah zai amsa daukacin adduo’inmu, ya kuma shawarci yan Nijeriya dasu kaucewa tashin hankali da ramuwar gayya. Wani babban Jami’in kungiyar Nigeria Prays, Moses Aransiola, shi ma ya bukaci yan Nijeriya su kara kaimi wajen adduo’in da suke yi, ya ce, kungiyar tayi matukar imani da addua a matsayin abinydaya zai ceto kasar nan yin addua kuma wani hakki ne na dukkan Kiristocin Nijeriya baki daya.

Ya kuma kara bayyana cewa, kungiyar ta dade tana gudanar da adduo’i a fadin kasar nan domin neman ci gaban kasa. Suna kuma karfafa kushin kasa da adalci da Shugabanci na gari a fadin kasar nan.

A sakonsa, shugaban kungiyar President, Pentecostal Fellowship of Nigeria” Felid Ya bukaci yan Nijeriya su rinka fadin gaskiya da maganganu na gari a kan kasa saboda Idan suka tsine wa kasa tsinuwar zai dawo kansu kai tsaye. Ya kuma tabbatar da cewa, Allah zai kawo wa kasar nan dauki domin samun Sabuwar Nijeriya. A gabatar da adduo’i da musamman ga Nijeriya da jihohi 36 na kasar nan.

 


Advertisement
Click to comment

labarai