Connect with us

LABARAI

Makarantar Nurul Hidaya Ta Gudanar Da Bikin Saukar Karatun Dalibai 44

Published

on


Makarantar Nurul Hidaya Islamiyya Kwasangwami dake Karamar Hukumar Gezawa ta gudanar da bikin saukar Karatun Alkur’ani na Dalibai 44 hudu, ashirin da uku maza da kuma mata 21 karo na uku. Da yake gabatar da jawabin maraba wakilin shugabar sashin ilimi na Karamar Hukumar Gezawa ya bayyana farin cikinsu bisa amsa gayyatar da jam’a da suka yi, saboda haka sai ya bukaci jama’a da suka mai da hankali wajen tarbiyar yara tare da bayar da dukkan hadin kan da malamai ke bukata wajen gudanar da harkokin koyarwa.

Shugaban Makarantar Nurul Hidaya Malam Adamu Abdullahi ana sa jawabin ya fara bayyana kadan daga cikin Tarihin Makarantar wadda yace an kafa Makarantar A shekara 2008 da dalibai 18 da  malami guda daya, amma cikin jinkan Allah yau gashi makarantar na da Daliban da suka haura 1,118, ya ce shekara 2010 ne Makarantar ta samu rijista da hukumar ilimi ta karamar hukumar Gezawa kuma aka turo malamin hukuma guda daya domin ci gaba da bayar da ilimi.

Malam Adamu Abdullahi ya ci gaba da cewa yau kuma alhamdulillahi gashi ana gudanar da bikin saukar Karatun Dalibai 44 maza da mata, wannan ya tabbatar da gagarumar nasarar da ake fata tun lokacin kafuwar wannan Makaranta. Shugaban ya kuma jinjinawa Mai girma Hakimin Gezawa Mai Unguwar Mundubawa Alhaji Muhammadu Yusufu bisa kyakkyawar kulawar da yake baiwa harkokin da suka shafi addini. Haka kuma a lokacin bikin saukar karatun shugaban makarantar ya yiwa Jama’a tanbihin gudumawar da wakilin al’ummar Gabasawa da Gezawa a Majalisar wakilai ta tarayya Honarabul Musa Ado Tsamiya Babba bisa samar da rijiyar burtsatse tare da yiwa Malamai da dalibai kyaututtuka iri daban daban.

Da yake gabatar da nasa Jawabin Hakimin Gezawa Mai unguwar Mundubawa Alhaji Muhammadu Yusufu ya bayyana farin cikinsa bisa ganin yadda wadannan dalibai suka yi dacen sauke alkur’ani, yace garin Gezawa garin Malamai ne saboda haka duk wani al’amarin alkur’ani bana  mamaki idan an  same shi yankin Gezawa, saboda haka sai ya yi addu’a tare da taya murna ga wadannan dalibai da Allah ya horewa samun saukar alkur’ani, daga nan sai ya  hori jama’a da su kara kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma yin kyakkyawan tunani aduk wani al’amarin rayuwa.

Alhaji Aminu Dan Jummai Kwasargwami wanda ya wakilci Honarabul Musa Ado Tsamiya Babba ya bayyana cewa ko shakka babu wannan makaranta tana cikin kahon zuciyar Dan Majalisar Wakilan mai wakilta al’ummar Gabasawa da Gezawa, domin kamar yadda aka sani wannan itace sauka karo na uku wanda kuma kowacce sauka da shi ake, wannan ma wani aikin kasa ne ya tsare shi, saboda haka ya umarce ni da cewar lallai na tabbatar da ganin mun halarci wannan saukar alkur’ani, kuma kamar yadda kowa ya ji aikinsa kadai ake iya gani a wannan makaranta, saboda haka muna tabbatarwa da jama’a cewar da yardar Allah zamu isar da dukkan sakon da ake fatan isarwa Alhaji Musa Ado Tsamiya Babba.

Shugaban gidauniyar Ganduje Alhaji Rabiu Jafar alokacin da yake taya wadannan dalibai murnar sauke alkur’ani bisa, sannan kuma ya gabatar da gudunmawar alkur’anai guda 44 domin rabawa daliban da suka sauke alkur’anin, haka kuma shugaban gidauniyar Ganduje ya tabbatwa da jama’a aniyar Gwamnatin Ganduje na ci gaba da kwararo ayyukan alhairi ga Kanawa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai